Dalilina na amincewa da gagarumin garambawul ga hukumar NYSC – Tinubu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, ya bayyana cewa gwamnatin sa ta amince da gagarumin garambawul ga tsarin Hukumar Yi Wa ƙasa Hidima ta Matasa (NYSC) ne domin bai wa matasan Nijeriya ƙwarewar aiki mai amfani, inganta hidimar ƙasa da kuma shirya su yadda za su taka muhimmiyar rawa wajen bunƙasa ƙasar.

An amince da waɗannan sauye-sauyen ne a zaman Majalisar Zartarwa ta Tarayya (FEC) da aka gudanar ranar Litinin.

Shugaban ƙasar ya bayyana cewa wannan shi ne mafi girman sauyi da aka taɓa yi wa shirin NYSC tun bayan kafa shi a shekarar 1973, kuma yana daga cikin alƙawurran gwamnatin sa na samar wa matasa damammaki masu amfani.

Tinubu ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da ya wallafa a shafinsa na ɗ ranar Laraba, inda ya ce garambawul ɗin ya cika ɗaya daga cikin manyan alƙawurran da ya ɗauka lokacin da ya karɓi ragamar mulkin ƙasar.

Ya ce, “A ranar Litinin, Majalisar Zartarwa ta Tarayya ta amince da mafi girman sauye-sauye ga tsarin NYSC tun bayan kafa shi a shekarar 1973.

“A ranar da na rantse a matsayin Shugaban ƙasa, na yi alƙawarin samar wa matasan Nijeriya damammaki masu amfani. Na kuma yi alƙawarin cewa mata da matasa za su kasance a sahun gaba a gwamnatinmu, kuma wannan garambawul wani ɓangare ne na cika wannan alƙawari.”

Shugaban ƙasar ya amince cewa tsawon shekaru 53, shirin NYSC ya taka muhimmiyar rawa wajen ƙarfafa haɗin kan ƙasa, amma ya ce yanayin Nijeriya na yau ya sa dole shirin ya faɗaɗa manufarsa domin shirya matasa yadda za su dace da ƙalubale da buƙatun zamani.

A cewarsa, matasa sun kai kusan kashi 70 cikin 100 na al’ummar Nijeriya, don haka ba nauyi ba ne, illa su ne ginshiƙin ci gaban ƙasar.

Tinubu ya sanar da cewa daga yanzu shirin tantancewa da horaswar farko (Orientation Camp) zai ɗauki makonni shida maimakon yadda ake yi a baya.

Ya ce, sabon tsarin karatun zai mayar da hankali kan tarbiyyar ɗan ƙasa, jagoranci, ɗabi’u na gari, shirye-shiryen shiga kasuwar aiki, kasuwanci, ilimin fasahar zamani, ilimin tafiyar da kuɗi da kuma horaswa ta musamman da za ta dace da fannin karatu da burin aikin kowane ɗan yi wa ƙasa hidima.

Shugaban ƙasar ya ƙara da cewa za a horas da masu yi wa ƙasa hidima a fannoni da suka haɗa da noma, lafiya, ilimi, fasaha, shari’a, aikin gwamnati, gine-ginen more rayuwa, tattalin arzikin kore, harkokin kasuwanci, masana’antun ƙirƙira da kuma ayyukan tsaro da na rundunonin sa-kai.

Ya ce manufar ita ce tabbatar da cewa duk wanda ya kammala shirin NYSC ya fita da ƙwarewar da za ta taimaka masa wajen samun aiki, kafa sana’a da kuma hidimtawa ƙasa.

Game da tsaron masu yi wa ƙasa hidima, Tinubu ya ce sabon tsarin zai yi amfani da tantance haɗarin tsaro kafin tura matasa zuwa wuraren hidima, musamman a jihohin da ke fama da matsalolin tsaro.

Ya bayyana cewa za a fi bai wa ‘yan asalin jihohin, mazauna jihohin, waɗanda suka kammala karatu a cibiyoyin ilimi na jihohin da abin ya shafa da kuma waɗanda suka fito daga jihohin maƙwabta cikin shiyyar siyasa ɗaya fifiko wajen tura su.

Har ila yau, ya ce tsarin kiran masu yi wa ƙasa hidima zai koma na zamani ta hanyar amfani da fasaha, yayin da wuraren aikin da za a tura su za su kasance masu dacewa da fannin karatunsu, ƙwarewarsu da kuma burinsu na sana’a.

Dangane da tafiyar da hukumar, Shugaban ƙasar ya bayyana cewa daga yanzu farar hula ce za ta jagoranci NYSC a matsayin Darakta Janar, tare da mataimakan Daraktocin Zartarwa uku, ciki har da Daraktan Zartarwa mai kula da harkokin tsaro wanda zai fito daga rundunar soji ko wata hukumar tsaro ta sa-kai.

Ya kuma bayyana cewa za a dinga tantance sansanonin horaswar NYSC bisa sabon tsarin ƙasa na kimantawa da bayar da shaidar inganci, yayin da gwamnatocin jihohi za su kasance wajibi su cika ƙa’idojin gudanar da sansanonin. Tinubu ya ce daga yanzu bikin yaye masu yi wa ƙasa hidima ba za a ƙara kiransa Passing-Out Parade ba, sai dai Bikin Kammala Karatun NYSC, domin masu hidimar za su kammala shirin ne a matsayin matasa masu ilimi da ƙwarewar sana’a da za su ba da gudummawa ga ci gaban ƙasa.

Shugaban ƙasar ya yabawa Ministan Raya Matasa, Ayodele Olawande, Mai Ba Shugaban ƙasa Shawara ta Musamman kan Manufofi da Daidaita Ayyuka, Hadiza Bala Usman, Ma’aikatar Ilimi ta Tarayya da kuma kwamitin da ya tsara garambawul ɗin bisa gudummawar da suka bayar. Sannan ya umarci Ma’aikatar Raya Matasa ta Tarayya da Ma’aikatar Shari’a ta Tarayya da su fara gyaran Dokar NYSC da sauran ƙa’idojinta domin bai wa waɗannan sauye-sauye cikakken ƙarfin doka.

A ƙarshe, Tinubu ya yi kira ga matasan Nijeriya da su ci gaba da yarda da makomar ƙasarsu.

Ya ce, “Nijeriya ta yarda da ku. Muna gina ƙasar da ta dace da baiwarku, burinku da kuma makomarku.”

By ukarofi

Leave a Reply