Daga MAHDI MISA MUHAMMAD
Babban Bankin Nijeriya (CBN) ya soke lasisin wasu bankunan gudanar da harkokin bayar da lamuni ga ƙananan masu sana’o’i guda 46 a faɗin ƙasar nan, sakamakon gaza cika muhimman ƙa’idojin da hukumar ke shimfiɗawa. A cikin wata sanarwa da Muƙaddashiyar Daraktar Sashen Sadarwar Kamfanoni ta CBN, Malama Hakama Sidi-Ali, ta fitar a ranar Laraba, bankin ya bayyana cewa matakin ya fara aiki nan take.
CBN ta ce ta ɗauki wannan mataki ne bisa ikon da Sashe na 12 da na 13 na Dokar Bankuna da Sauran Cibiyoyin Kuɗi (BOFIA), 2020 suka ba ta, bayan gano manyan take haƙƙin dokokin banki da bankunan suka aikata.
Babban Bankin ya bayyana cewa bankunan da abin ya shafa sun kasa cika sharuɗɗan da ake buƙata domin ci gaba da gudanar da aiki a matsayin cibiyoyin kuɗi masu lasisi.
A cewar CBN, binciken sa ido da take gudanarwa akai-akai ya gano cewa bankunan sun dade suna karya dokokin banki ba tare da gyara ba, lamarin da ya sa dole aka janye lasisinsu.
Bankin ya ƙara da cewa wannan mataki na daga cikin ƙoƙarinsa na ƙarfafa amincewar jama’a da tsarin banki tare da tabbatar da cewa cibiyoyin kuɗi masu ƙarfi da bin doka ne kawai ke ci gaba da aiki.
Daga cikin laifukan da aka gano akwai rashin isassun kadarori da za su iya biyan basussuka, daina gudanar da harkokin banki na tsawon lokaci, dakatar da ayyuka ba tare da amincewar hukuma ba, gaza fara aiki cikin watanni 12 bayan samun lasisi, da kuma kasa riƙe mafi ƙarancin jarin da doka ta tanada saboda asarar da suka yi. CBN ta bayyana cewa waɗannan matsaloli sun hana bankunan cika nauyin da ya rataya a wuyansu a matsayin cibiyoyin kuɗi masu lasisi.
Babban Bankin ya ce manufar soke lasisin ita ce kare tsarin kuɗi na ƙasa da kuma tabbatar da tsaron kuɗaɗen masu ajiyar kuɗi. Sanarwar ta ce:, “Soke waɗannan lasisai na daga cikin matakan da Babban Bankin Nijeriya ke ɗauka domin tabbatar da dorewar tsarin kuɗi, kare masu ajiya da kuma tabbatar da cewa cibiyoyin kuɗi masu lasisi suna bin dokoki da ƙa’idojin da ake aiki da su.”
CBN ta kuma sake tabbatar da aniyarta na gina tsarin kuɗi mai ƙarfi, aminci da juriya, tana mai cewa za ta ci gaba da ɗaukar duk matakan sa ido da suka dace domin kare martabar harkokin banki a Nijeriya.
Har ila yau, bankin ya fitar da cikakken jerin sunayen bankunan bayar da lamuni ga ƙananan masu sana’o’i guda 46 da aka soke wa lasisi, lamarin da ke nufin sun daina gudanar da aiki a hukumance a Nijeriya.
