Daga JAMIL GULMA a Kebbi
Kakakin majalisar dokokin jihar Legas Mudashiru Ajaiye Obasa ya gana da shugabannin al’ummar Arewa ƴaƴan jam’iyyar APC mazauna Legas reshen Agege ƙarƙashin jagorancin Alhaji Sa’adu Yusuf Ɗandare Gulma.
Da ya ke jawabi, Alhaji Obasa ya nuna jin daɗin sa bisa ga amsa goron gayyatar da ya yi sannan ya bayyana cewa akwai buƙatar a haɗa hannu tare domin a gudu tare a tsira tare.
Ya zama wajibi ga dukkan mu da mu natsu mu kalli matsalolin da ke dabaibaye da mu, mu magance su domin samun siyasa mai tsafta duk da bambance-bambancen yare da al’adu da ke tsakanin mu.
A matsayin sa na shugaba dole ne na yi kuskure wanda bai kamata a rinƙa kallon sa yana tafiya kan kuskuren ba ba tare an yi masa gyara ba, saboda ana tafiya tare ne a ƙarƙashin Jam’iyyar APC duk da bambance-bambancen yare da al’adu.
Akwai nauyi da ya rataya a kan mu duka shugabanni na gano matsalolin al’ummar da mu ke waƙilta tare da magance su.
Da ya ke jawabi Alhaji Sa’adu Gulma ya bayyana cewa al’ummar Arewa mazauna Legas a ƙarƙashin jagorancin sa a shirye su ke da su bayar da goyon baya ga duk abinda zai kawo cigaba.
Ya kuma yaba wa Kakakin majalisar bisa ga sauraron su da ya ke yi a duk lokacin da buƙatar hakan ta taso.
