Gwamnan Kebbi ya jajanta wa shugaban hukumar Sokoto Rima River Basin

Spread the love

Daga JAMIL GULMA a Kebbi

Gwamnan jihar Kebbi Malam Nasir Idris ya jajanta wa shugaban hukumar Sokoto Rima Basin Authority Alhaji Abubakar Gari Malam bisa ga iftila’in gobara da ta ƙone gidan sa da ke garin Birnin Kebbi daren jiya.
Malam Nasir Idris bayan jimamin lamarin ya bayyana wannan iftila’i a matsayin hukuncin Allah ne da ba wanda zai iya hana afkuwar haka.
Ya ce a madadin sa da ilahirin al’ummar jihar Kebbi suna jejanta masa.
Ya kuma ba shi haƙuri tare da fatan mayar da lamarin ga Allah da kuma addu’ar Allah ya mayar masa fiye da abinda ya rasa duk da ya ke dai ba a sami hasarar rayuwa ba amma dai an samu asarar dukiya mai yawa.

Ya yi kira ga al’umma da su kiyaye da duk kayan da su ke amfani da su wajen girki musamman irin kayan zamani da suka shafi gas.

By ukarofi

Leave a Reply