Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Hukumar Kula da Tsarin Wutar Lantarki ta Nijeriya (NERC) ta bayyana cewa, Kamfanonin Rarraba Wutar Lantarki (DisCos) sun karɓi jimillar Naira biliyan 203.61 daga hannun masu amfani da wutar lantarki a watan Afrilu. Rahoton ya fito ne cikin Takardar Bayanai Kan Ayyukan Kasuwanci, wato Commercial Performance Factsheet, ta baya-bayan nan da hukumar ta fitar.
Rahoton ya nuna cewa kuɗin da kamfanonin suka tara a watan Afrilu ya zarce Naira biliyan 196.13 da aka tattara a watan Maris, lamarin da ke nuna ƙarin kashi 3.8 cikin 100 na kuɗaɗen shiga da kamfanonin rarraba wutar lantarki 11 na ƙasar suka samu.
A cewar NERC, darajar wutar lantarkin da kamfanonin suka karɓa daga masu samar da wuta ta kuma ƙaru daga Naira biliyan 293.76 a watan Maris zuwa Naira biliyan 302.96 a watan Afrilu.
Haka kuma, rahoton ya nuna cewa darajar kuɗin wutar lantarkin da aka caji masu amfani da ita ta kai Naira biliyan 252.43 a watan Afrilu, idan aka kwatanta da Naira biliyan 246.43 da aka yi wa kwastomomi lissafi a watan Maris.
Hukumar ta ce kamfanonin sun samu ƙimar karɓar kuɗin da aka caji ta kashi 80.66 cikin 100 a watan Afrilu, wanda ya fi kashi 79.59 cikin 100 da aka samu a watan Maris da maki 1.07.
Sai dai NERC ta lura da ɗan raguwar ƙimar cajin kuɗin wuta yadda ya kamata, wato billing efficiency, wadda ta sauka zuwa kashi 83.32 cikin 100 a watan Afrilu daga kashi 83.89 cikin 100 da aka samu a watan da ya gabata.
Rahoton ya kuma nuna cewa kamfanonin sun samu ƙimar dawo da kuɗaɗen shiga ta kashi 82.11 cikin 100, inda matsakaicin kuɗin da suka karɓa ya kai Naira 102.13 kan kowace kilowatt-awa (kWh), yayin da farashin da aka amince da shi ya kasance Naira 124.39 kan kowace kilowatt-awa.
A fannin ƙwarewar dawo da kuɗaɗen shiga, Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Eko (EKEDC) ne ya kasance kan gaba, bayan ya samu ƙimar kashi 102.09 cikin 100.
Kamfanin Rarraba Wutar Lantarki na Abuja (AEDC) ya zo na biyu da kashi 89.77 cikin 100, yayin da Kamfanin Ikeja ya zo na uku da kashi 88.89 cikin 100.
NERC ta bayyana cewa waɗannan kamfanoni uku ne suka fi sauran kamfanonin rarraba wutar lantarki 11 na Najeriya ƙwarewa wajen dawo da kuɗaɗen shiga a watan Afrilu, abin da ke nuna ci gaba a ayyukan kasuwanci a fannin rarraba wutar lantarki a kasar.
