Nijeriya ta buƙaci ’yan kasuwa su rage farashi bayan faɗuwar ɗanyen mai

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Gwamnatin Tarayya ta buƙaci masu harkar sayar da man fetur su daidaita farashin fetur da sabon yanayin kasuwar duniya, bayan da farashin ɗanyen mai ya ragu sakamakon sassauta rikicin da ya dabaibaye ƙasashen Iran da Amurka.

ƙaramin Ministan Albarkatun Man Fetur Mai Kula da Harkokin Mai, Sanata Heineken Lokpobiri, ne ya bayyana hakan a Abuja yayin taron masu ba da shawara kan harkokin shari’a da Hukumar Kula da Haƙowa da Tace Man Fetur ta Nijeriya ta shirya a shekarar 2026.

Kiran na zuwa ne a daidai lokacin da masu amfani da man fetur da wasu masu ruwa da tsaki ke zargin dillalan mai da ci gaba da cin gajiyar jama’a duk da raguwar farashin ɗanyen mai a kasuwannin duniya.

Lokpobiri ya ce, bayan raguwar zaman ɗar-ɗar da ta biyo bayan rikicin Iran da Amurka, ana sa ran farashin ɗanyen mai a duniya zai sauka, wanda ya kamata ya haifar da raguwar farashin fetur da sauran kayayyakin man fetur a cikin gida.

“Bayan sassautuwar rikicin Iran da Amurka, mun yi tsammanin za a ga raguwar farashin fetur da sauran kayayyakin man fetur daidai da yadda farashin ɗanyen mai ya sauka. Amma har yanzu hakan bai faru yadda ya kamata ba,” inji ministan.

Sai dai ya jaddada cewa tun bayan aiwatar da tsarin ’yantar da kasuwar man fetur ƙarƙashin Dokar Masana’antar Man Fetur ta 2021, gwamnati ba ta da ikon ƙayyade ko rage farashin fetur kai tsaye. A cewarsa, ƙarfin kasuwa, gasa, samarwa da buƙata ne yanzu ke ƙayyade farashin fetur a gidajen mai.

Duk da haka, ya ce Hukumar Kula da Haƙowa da Tace Man Fetur na da alhakin sa ido kan masu gudanar da harkar domin tabbatar da cewa ba a cutar da masu amfani da kayayyakin man fetur ba ta hanyar tsadar da ba ta dace ba.

Ministan ya bayyana cewa, tsarin ’yantar da kasuwar ya samar da gagarumin ci gaba a ɓangaren man fetur, ciki har da ƙaruwar wadatar kayayyaki da kuma zuba jari a matatun mai na cikin gida. Ya ce, tsarin ne ya samar da yanayin da ya ba da damar fara aiki a matatar Dangote tare da ƙarfafa sauran ayyukan gina matatun mai a faɗin ƙasar.

Lokpobiri ya kuma ce matsalar ƙarancin man fetur da aka saba fuskanta a baya ta ragu sosai, yana mai cewa tun daga shekarar 2023 ’yan Nijeriya na samun wadataccen fetur duk da matsalolin da rikice-rikicen siyasa suka haifar a kasuwannin duniya.

A nasa jawabin, Babban Jami’in Gudanarwa na hukumar, wanda Daraktan Tsarin Rarrabawa, Ajiya da Kayayyakin Dillanci, Rabiu Abdullahi Umar ya wakilta, ya ce aiwatar da Dokar Masana’antar Man Fetur ta shiga sabon mataki, inda hankali ya koma daga tsara dokoki zuwa tabbatar da aiwatar da su yadda ya kamata. Ya ce masu tsara dokoki, lauyoyi da masu ba da shawara ga kamfanoni na da muhimmiyar rawa wajen tabbatar da bin doka da kuma ƙarfafa amincewar masu zuba jari a masana’antar man fetur.

Haka kuma, Sakataren Hukumar kuma Mai Ba Da Shawara Kan Harkokin Shari’a, Dakta Joseph Tolorunse, ya ce tabbatar da tsayayyen tsarin doka yana da matuƙar muhimmanci wajen jawo zuba jari da ci gaban masana’antar.

By ukarofi

Leave a Reply