Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD
Asusun Lamunin Karatun ɗalibai na Nijeriya (NELFUND) ya nuna damuwa kan rahotannin da ke nuna cewa wasu manyan makarantun gaba da sakandare na ƙasar nan suna jinkirta ko kuma ƙin mayar wa ɗaliban da suka riga suka biya kuɗin makaranta kuɗaɗensu bayan an biya musu kuɗin karatu ta shirin lamunin ɗalibai.
A cikin wata sanarwa da Daraktan Sadarwa da Hulɗa da Jama’a na NELFUND, Oseyemi Oluwatuyi, ya sanya wa hannu a ranar Litinin, asusun ya kuma yi tir da yadda wasu makarantu ke ƙara kuɗin makaranta da sauran kuɗaɗen gudanarwa ba tare da wani tsari ko dalili karɓaɓɓe ba.
Sanarwar ta bayyana cewa shirin lamunin ɗalibai, wanda gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu ta ƙaddamar, an samar da shi ne domin rage matsalolin kuɗi da ke hana matasa samun ilimi a manyan makarantu, ba wai domin ƙara ɗora musu wasu nauye-nauye ba.
NELFUND ta ce ta lura da rahotannin da ke nuna cewa wasu cibiyoyin ilimi suna jinkirta mayar da kuɗin makaranta ga ɗaliban da suka cancanta, duk kuwa da cewa an riga an tura musu kuɗin karatunsu ta hanyar shirin lamuni.
Hukumar ta bayyana cewa tana tattaunawa da makarantun da abin ya shafa tare da sauran hukumomin da ke da ruwa da tsaki domin tabbatar da cewa an mayar wa ɗaliban da suka cancanta kuɗaɗensu cikin gaggawa.
Haka kuma, ta jaddada cewa za ta yi aiki domin tabbatar da cewa kuɗaɗen makaranta da sauran kuɗaɗen da cibiyoyin ilimi ke karɓa sun kasance masu adalci, bayyanannu kuma sun yi daidai da manufofin da aka kafa shirin lamunin ɗalibai a kansu.
A cewar NELFUND, ƙarin kuɗaɗen makaranta ba bisa ƙa’ida ba da kuma ƙin mayar da kuɗin ɗalibai na iya kawo cikas ga nasarar wannan muhimmin shiri na ƙasa wanda aka samar domin tallafa wa ɗalibai masu ƙaramin ƙarfi.
Asusun ya sake tabbatar da aniyarsa ta kare muradun ɗalibai tare da kiyaye martaba da gaskiyar wannan babban shiri na tallafin ilimi da gwamnatin tarayya ta ƙaddamar.
Masu sa ido kan harkokin ilimi na ganin cewa wannan gargaɗi da NELFUND ta yi na zuwa ne a daidai lokacin da ɗalibai da dama ke ƙorafin cewa wasu makarantu sun kasa mayar musu da kuɗaɗen da suka riga suka biya kafin samun amincewar lamunin karatunsu.
