
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Babbar Kotun Jihar Kaduna ta yi watsi da buƙatar beli da tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya gabatar, bayan Asibitin Ƙasa da ke Abuja ya musanta rahoton lafiyar da aka gabatar domin tallafa wa buƙatar.
Rahotanni sun bayyana cewa, an miƙa rahoton lafiyar ne a matsayin hujja don neman a bada belin El-Rufai, amma Asibitin Ƙasa ya bayyana cewa rahoton ba daga gare shi ya fito ba, lamarin da ya jefa sahihancinsa cikin shakku.
Hukumar ICPC a wata sanrwa, ta ce tsohon gwamnan ya gabatar da rahoton lafiyar ne a matsayin hujjar buƙatar belin nasa da aka ce an amso ne daga babban asibitin.
A cewar ICPC, rahoton lafiyar ya yi iƙirarin cewa an binciken cutar daji mai ƙarfi akan tsohon gwamnan da ke buƙatar a gaggauta ɗaukar matakin magani a kai.
Bayan nazarin bayanan da aka gabatar, kotun ta hannun Alƙali Darius Khobo, ta yanke hukuncin yin watsi da sabuwar buƙatar belin, tare da cigaba da bin hanyoyin shari’a kamar yadda doka ta tanada.
