Gwamnatin Zamfara ta yaba wa Shugaban NAHCON kan nasarar ayyukan Hajjin 2026

Spread the love

Daga BELLO A. BABAJI a Abuja

Gwamnatin Jihar Zamfara ta jinjina wa Shugaban Hukumar Jigilar Alhazan Nijeriya (NAHCON), Ambasada Isma’il Abba Yusuf bisa ƙoƙarinsa wajen tabbatar da cimma nasarorin ayyukan Hajjin 2026 da ya gudana.

A wata takarda da hukumar gudanarwar NAHCON ta fitar a ranar Juma’a, an bayyana cewa wata tawaga daga gwamnatin jihar ƙarƙashin jagorancin Daraktan Filin jiragen sama na Gusau, Alhaji Kabiru Yahaya Gusau ne ta bayyana haka yayin ziyartar ga Ambasada Isma’il Abba a ranar Alhamis.

Daga cikin ‘yan tawagar da Gwamna Dauda Lawal ya aike akwai Darakta kuɗi da rabawa, Alhaji Yahuza Mai Haja; Daraktan Fasahar Labarai da Sadarwa na Hukumar Tattara Harajin Zamfara, Alhaji Bilyaminu Ahmad Muhammed; da kuma Jami’in tattara haraji, Alhaji Anas Muhammed Gusau.

Da yake jawabi a madadin ‘yan tawagar, Alhaji Kabiru Yahaya Gusau ya isar da saƙon gwamnan na yaba wa Ambasadan musamman akan ƙoƙarin ma’aikata, hukumomin jigilar alhazai na jihohi da sauran masu ruwa da tsaki.

Tawagar ta kuma yaba da salon dabarun shugabancin Abba Yusuf a hukumar da kuma nuna gamsuwa da hidimarta a ƙarƙashinsa, tana mai fatan a samu ɗorewa akan haka.

A ƙarshe, an yi addu’ar neman cigaba da samun nasarori ga NAHCON da kuma fatan samun ƙarin haɗin-gwiwa a tsakaninta da gwamnatin Zamfara akan lamuran aikin hajji.

By Babaji

Leave a Reply