Babbar badaƙala: Gwamnati ta fallasa hukumar bogi

Spread the love

*Har an saka ta a kasafin kuɗin Gwamnatin Tarayya

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja 

Fadar Shugaban ƙasar Nijeriya ta bayyana cikakken bayani kan yadda wani mutum mai suna Adeniyi Adeyemi Matthew ya ƙirƙiri wata hukumar gwamnatin tarayya ta bogi, ya buɗe ofis a Sakatariyar Tarayya da ke Abuja, tare da gabatar da kansa a matsayin Darakta Janar domin gudanar da ayyukan da ba su da sahalewar gwamnati.

A cikin wata sanarwa da Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara kan Yaɗa Labarai da Dabarun Aiki, Mista Bayo Onanuga, ya fitar, ya ce babu wata hukuma mai suna Presidential Foreign Intervention Promotion Council (PFIPC) ko Presidential Economic Advisory Council da gwamnatin tarayya ta kafa, sannan Ofishin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa bai taɓa ba Adeyemi takardar naɗi ba.

Sanarwar ta ce zargin ya fara bayyana ne bayan Hukumar Bunƙasa Zuba Jari ta Nijeriya (NIPC) ta sanar da Fadar Shugaban ƙasa cewa akwai wata ƙungiya da ke gudanar da ayyuka kamar hukuma ta gwamnati, duk da cewa ba ta da wata doka ko amincewa.

Binciken da aka gudanar ya nuna cewa Adeyemi ya buɗe ofis a hawa na biyu na Federal Secretariat Phase III da ke Abuja, inda yake karɓar baƙi tare da gabatar da kansa a matsayin Darakta Janar na wata hukuma ta bogi.

Fadar Shugaban ƙasa ta kuma ce Adeyemi da abokan hulɗarsa sun riƙa shirya tarurruka da jakadun ƙasashen waje da sauran masu ruwa da tsaki, suna iƙirarin cewa suna wakiltar gwamnatin Nijeriya.

An ce a ranar 10 ga Oktoban 2025, ya shirya wani taro a Wells Carlton Hotel da ke Asokoro, Abuja, inda ya gayyaci jakadun ƙasashen waje ba tare da izini ko sanin Ma’aikatar Harkokin Waje ba.

Bayan wannan taro, Ma’aikatar Harkokin Waje ta aika wasiƙa ranar 15 ga Oktoba, 2025, tana bayyana cewa taron ya saɓa wa ƙa’idojin hulɗar diflomasiyya, tare da neman bayani daga Ofishin Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara kan Tsaro da kuma Ofishin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa.

A cewar sanarwar, tun kafin wannan wasiƙa, Ofishin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa ya kai ƙorafi ga Hukumar DSS da kuma Rundunar ‘Yan Sanda ta Nijeriya a ranar 17 ga Oktoba, 2025, bayan gano cewa ana amfani da takardun naɗi na bogi masu ɗauke da sa hannu, tambari da lambobin gwamnati na ƙarya.

An kuma gano cewa Adeyemi ya nemi Ma’aikatar Harkokin Waje ta fitar masa da takardar diflomasiyya (Note Verbale) domin samun bizar Amurka ga shi da waɗanda ya kira ma’aikatansa.

Sanarwar ta ce an haɗa kwafen takardun bogin, buƙatun biza da hotunan da aka samu daga shafin intanet na hukummar bogin a cikin ƙorafin da aka kai wa jami’an tsaro.

Fadar Shugaban ƙasa ta jaddada cewa Ofishin Shugaban Ma’aikata ba shi da ikon ƙirƙirar hukumomin gwamnati ko bayar da takardun naɗi, domin wannan na cikin ikon Ofishin Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF).

Bayan bincike, jami’an ‘yan sanda sun kama Adeyemi a ranar 27 ga Oktoba, 2025, a ofishin da yake gudanar da ayyukan bogin a Sakatariyar Tarayya.

An ce binciken da aka yi a ofishinsa da gidansa da ke Suleja ya gano takardun bogi da sauran kayayyakin da ake zargin an yi amfani da su wajen aikata laifin.

Fadar Shugaban ƙasa ta ce yayin tambayoyi, Adeyemi ya yi iƙirarin cewa wani Dolapo Babatunde Tanimola ne ya taimaka masa wajen samar da takardar naɗin bogin. Sai dai binciken ‘yan sanda ya nuna cewa mutumin ya rasu ne a gobarar da aka yi a wani otel a Abuja kwanaki biyar kafin a kama Adeyemi.

Haka kuma binciken ya gano cewa Adeyemi na da asusun banki guda 34, ciki har da guda tara da aka buɗe da sunayen hukumomin gwamnati na bogi.

An kuma zarge shi da buɗe asusun Babban Bankin Nijeriya (CBN) ta hanyar yaudarar Ofishin Akanta Janar na Tarayya, ko da yake bincike ya tabbatar da cewa ba a taɓa zuba kuɗin gwamnati a cikin asusun ba.

Bayan kammala bincike, Rundunar ‘Yan Sanda ta gurfanar da Adeyemi da wasu mutum biyu a gaban Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja bisa tuhume-tuhume takwas a ranar 27 ga Nuwamba, 2025. Ana sa ran kotun za ta ci gaba da sauraron shari’ar a ranar 27 ga Yulin 2026.

Fadar Shugaban ƙasa ta kuma yi zargin cewa bayan an ba shi beli, Adeyemi ya sake fitowa yana iƙirarin cewa Ofishin Shugaban Ma’aikatan Fadar Shugaban ƙasa ne ya naɗa shi, duk da cewa ya musanta hakan lokacin da ‘yan sanda suka yi masa tambayoyi.

A ƙarshe, Fadar Shugaban ƙasa ta buƙaci ‘yan siyasa da sauran jama’a su bari kotu ta yanke hukunci kan lamarin, maimakon yaɗa bayanan da ta bayyana a matsayin ƙarya kafin fara shari’ar.

A wani martani da tsohon Ministan Wasanni, Solomon Dalung ya yi, ya buƙaci gwamnati ta yi ƙarin bayani kan zargin kafa hukumar bogin.

Tsohon Ministan Matasa da Wasanni na Nijeriya, Solomon Dalung, ya bayyana cewa sanarwar da Mai Bai wa Shugaban ƙasa Shawara na Musamman kan Yaɗa Labarai da Dabaru, Bayo Onanuga, ya fitar a madadin Fadar Shugaban ƙasa game da zargin da ya shafi Prince Adeyemi, ba ta warware dukkan tambayoyin da jama’a ke yi ba.

A cikin wata sanarwa da ya wallafa, Dalung ya ce a maimakon sanarwar ta daƙile ce-ce-ku-cen da ake yi, ta ƙara haifar da sababbin tambayoyi kan yadda ake gudanar da harkokin gwamnati.

Ya ce ko da za a ɗauka cewa dukkan zarge-zargen da ake yi wa Prince Adeyemi gaskiya ne, har yanzu akwai manyan giɓi da gwamnatin ba ta yi cikakken bayani a kansu ba.

Dalung ya ce abin mamaki ne yadda ake zargin mutum guda ya ƙirƙiri wata hukuma ta Fadar Shugaban ƙasa, ya ƙirƙiri takardar naɗin aiki, ya samu ofishi a Federal Secretariat, ya ɗauki ma’aikata, ya gudanar da tarurruka da jami’an diflomasiyya, ya yi mu’amala da hukumomin gwamnati, har ma ake zargin ya buɗe asusu a Babban Bankin Nijeriya (CBN), sannan kuma sunan hukumar ya bayyana a cikin kasafin kuɗin ƙasa tare da ware mata biliyoyin naira.

A cewarsa, idan hakan gaskiya ne, to lamarin ya nuna akwai babban gazawa a tsarin hukumomin gwamnati, domin ya kamata a yi bayani kan yadda hakan ya kasance.

Dalung ya nuna damuwa kan yadda sanarwar Fadar Shugaban ƙasa ba ta yi bayani kan yadda hukumar da ake cewa ta bogi ce ta samu shiga cikin kasafin kuɗin ƙasa ba.

Ya tambayi wa ya saka sunan hukumar cikin kasafin kuɗi, wa ya tantance ta, wa ya amince da ita, da kuma dalilin da ya sa babu wanda ya gano cewa ba ta da wata doka ko sahihancin wanzuwa.

Haka kuma ya ce akwai buƙatar gwamnati ta yi cikakken bayani kan yadda aka samu ofishin da ake zargin hukumar ta yi amfani da shi a Federal Secretariat, wa ya ba da izini, tsawon lokacin da aka yi ana amfani da ofishin, da kuma jami’an gwamnati da suka yi hulɗa da waɗanda ke aiki a wurin.

Dalung ya kuma yi tsokaci kan batun mutuwar Dolapo Babatunde Tanimola, wanda Fadar Shugaban ƙasa ta bayyana a matsayin mutumin da ake zargin ya haɗa Prince Adeyemi da takardar naɗin aikin.

Ya ce kasancewar Tanimola ya rasu a gobarar wani otal kwanaki biyar kacal kafin a kama Adeyemi, ya sa akwai buƙatar jama’a su san ko an gudanar da binciken gawa (autopsy), binciken Coroner, da kuma abin da bincike ya gano game da mutuwarsa.

Tsohon ministan ya ce waɗannan ba hasashe ba ne ko ƙoƙarin ƙirƙirar makirci, illa tambayoyi ne da suka dace a yi domin tabbatar da gaskiya.

Dalung ya jaddada cewa ko da kotu ce za ta yanke hukunci kan ko Prince Adeyemi ya aikata laifi ko a’a, gwamnati kuma tana da alhakin bayyana yadda hukumominta suka yi mu’amala da abin da yanzu ake cewa ƙirƙirarrer hukuma ce.

Ya ce idan hukumar bogi ce, gwamnati ta bayyana yadda ta shiga cikin kasafin kuɗi; idan takardar naɗin aiki ta jabu ce, a bayyana yadda hukumomin gwamnati suka ci gaba da mu’amala da wanda aka ce an naɗa; idan kuma babu hannun wani jami’in gwamnati a lamarin, a fito da hujjoji da takardun da ke tabbatar da hakan.

A ƙarshe, Dalung ya ce ‘yan Nijeriya sun cancanci samun cikakkun bayanai da hujjoji, ba sanarwar manema labarai kaɗai ba, yana mai cewa har sai an yi cikakken bayani tare da gabatar da takardu da shaidu, wannan batu ba zai ƙare ba.

By ukarofi

Leave a Reply