An gano gawarwaki mutum 30 bayan harin ’yan ta’adda kan masallatai a Neja – Shugaban Borgu

Spread the love

Daga MAHDI MUSA MUHAMMAD

Kimanin mutane 30 ne suka rasa rayukansu sakamakon hare-haren da aka kai wa masu ibada a lokacin sallar Juma’a a ƙananan hukumomin Borgu na Jihar Neja, yayin da aka yi awon gaba da sama da mutum 60, a cewar Shugaban Ƙƙaramar Hukumar Borgu, Mohammed Abdullahi.

Abdullahi ya ce, maharan sun sace sama da mutum 60 daga masallatai daban-daban a ƙauyuka huɗu, yayin da suke gudanar da sallar Juma’a a ranar Juma’ar da ta gabata.

Wannan bayani ya zo ne bayan Shugaban ƙasar Nijeriya, Bola Ahmed Tinubu, ya yi Allah-wadai da sace ɗimbin masu ibadar, tare da umartar hukumomin tsaro da su gaggauta ceto mutanen da aka yi garkuwa da su.

Rahotanni sun ce hare-haren sun faru ne kusan lokaci guda a ƙauyukan Dekara, Kpenya, Sabon-Gida da Gidan-Zana, a lokacin sallar Juma’a.

Majiyoyi sun bayyana cewa maharan sun tilasta wa masu ibadar ficewa daga cikin masallatan, sannan suka tisa ƙeyarsu zuwa cikin daji.

Da yake tabbatar da faruwar lamarin a wata tattaunawa ta wayar tarho, Abdullahi ya ce adadin mutanen da aka yi garkuwa da su ya haura 60.

Ya ce, mazauna yankunan da abin ya shafa sun gano tare da binne gawarwakin kusan mutum 30 da aka kashe a lokacin harin ko kuma bayan an yi garkuwa da su.

“Bisa bayanan da nake da su, waɗanda aka yi garkuwa da su sun ɗan haura 60. Waɗanda aka kashe kuma sun kusa 30. Ko da yake sojoji sun isa wurin kuma sun dawo da zaman lafiya, wasu mutane sun tsere zuwa wuraren da suka fi aminci,” inji shi.

Shugaban ƙaramar hukumar ya ƙara da cewa maharan sun kona gidaje da dama a yayin harin, ciki har da gidan Hakimin Gundumar Dekara, Abubakar Umar.

Ya tabbatar da cewa an yi awon gaba da waɗanda abin ya shafa daga cikin waɗannan al’ummomi huɗu ne a daidai lokacin da suke gudanar da sallar Juma’a.

Bayan harin, rahotanni sun ce ɗaruruwan mazauna yankunan sun ranta a na kare zuwa New Bussa da kuma wasu sassan ƙasar Benin, bayan da ‘yan ta’addan suka yi barazanar kashe duk wanda ya ci gaba da zama a yankunan.

A nasa ɓangaren, Rundunar ’Yan Sandan Jihar Neja ta tabbatar da tura jami’an tsaro na haɗin gwiwa zuwa yankunan da abin ya shafa, domin farautar maharan tare da ƙoƙarin ceto sauran mutanen da aka yi garkuwa da su.

Daga bisani, maharan sun fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna mutanen da suka yi garkuwa da su, wanda aka yada shi a shafukan sada zumunta.

By ukarofi

Leave a Reply