Hajji kiran Allah!

Tare da NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

Ko da mutum ya na da lafiya da guzurin tafiya aikin hajji sai Allah ya sa da rabon zai gudanar da aikin. Aikin hajji da ke cikin rukunan musulunci biyar na da matsayin mai iko ya samu damar gudanar da shi sau ɗaya a rayuwa. Wasu kan samu dama duk shekara su je aikin hajji. Wani wanda ba shi da halin zuwa ko don rashin lafiya ko rashin guzuri har ƙarshen rayuwar sa ba shi da wani laifi.

A tarihi an samu bayanan yadda wasu kan ɗau haramar tafiya hajji da ƙafa su ɗau shekaru su na tafiya har wasu daga ciki su samu nasarar gudanar da aikin wasu kuma su tsaya a hanya har ya kai su ga zama ‘yan wata qasa shi kenan duk sauran jama’arsu ko ‘ya’yan su da ke tare da su sai su rikiɗe su zama mazauna wata ƙasa ta kan hanyar tafiya Makkah.

Haƙiƙa wasu rai ma kan yi halin sa yayin da su ke ƙoƙarin tafiya aikin hajjin. Misali daga nan Nijeriya wasu sun kama hanyar Makkah amma su ka tsaya a hanya su ka zama ‘yan Chadi ko Sudan. Ka ga irin waɗannan sai an yo dace a san asalin garuruwan da su ka fito don asalin matafiyan sun daɗe da rasuwa sai zuriyarsu da ta tashi a wata ƙasa.

A bara ma ko bariya mun samu labarin wani xan jihar Filato da ya samu zuwa Makkah a kan keke ko laulawa. Ba mamaki gwarzan ba ya yi hakan don rashin kuɗin jirgi ba ne sai wataƙila don jarraba yadda tafiyar za ta iya yiwuwa kan keke.

A tsohon zamani tafiya a kafa kan iya yiwuwa cikin sauƙi ɗaya cikin biyu. Abu na farko lokacin ba dokoki masu tsauri na ratsa ƙasashe ba tare da VISA ba.

Abu na biyu kuma da yana nan shi ne kasadar haɗuwa da miyagun iri kamar ‘yan fashi, varayi da ma namun daji. A sabon zamanin akwai dukkan walubale kama daga na ratsa ƙasashe, rashin tsaro da ma tsananin tsadar rayuwa hatta a can Makkah duk da akwai sassauci da na Allah ba sa ƙarewa.

A can wasu shekaru kuma akwai waɗanda su ka kawo shirin tafiya hajji ta mota. Wannan shiri ma na tattare da ƙalubale da ba mamaki gara ma mai niyya ya tara kuxin sa ya shiga jirgi cikin sa’a 4 ya sauka a ƙasa mai tsarki ya fi sauƙi.

Gaskiya na dai na jin kwanan zancen tafiya hajji ta mota. Kafin na faɗa kan darasin sosai na yadda kujerar hajji ta yi ɗan karen tsada musamman a nan Nijeriya don lamarin tsadar canjin dala zan qarfafa cewa ita wannan tafiya ta addini kan zama kiran Allah. Wani ba shi da gida ko mota kai koma abinci wadatacce a gidan sa amma sai dalili ya ratsa ka ga Allah ya kira shi don sauke wannan farali.

A gefe guda kuma wani za a iya ba shi kyautar kujerar amma sai ya zavi ya sayar don samun hasafin rayuwar gida. Ni kai na a wata shekara ina ganin 2008 ne na samu kujerar an kammala komai amma sai dai kash sai ofishin jakadancin Saudiyya ya rufe ba da VISA. Labarin da na samu a lokacin an je da kamar fasfo 100 ciki da nawa sai jami’in ofishin ya wabci wasu a ciki ya buga mu su VISA ya bar sauran.

Nawa ya na cikin waɗanda a ka bari ba VISA. A wannan lokacin na koyi darasi da ke nuna duk dama da mutum ya ke da ita ta tafiya aikin hajji ta indai ba ka gan ka a filin Arfa ba ka cigaba da addu’a Allah ya sa haƙiƙa ka amsa kira. Waɗanda su ka saba zuwa hajji ba za su rasa jin labaran waɗanda kan ɓata a Makkah har a sauko daga aikin ba tare da sun gudanar da shi ba.

Kun ga kenan sauka a birnin Makkah mai daraja ba lallai ne ga wasu su samu gudanar da hajji ba. Kazalika tafiya ba tare da sanin dokokin aikin ma na zama wani ƙalubalen. Tun a ziyarar Madina gabanin shiga aikin hajji wasu kan koma ga Allah. Irin wannan sai ladar niyya. Ya na da daɗi ainun mutum ya samu gudanar da aikin hajji a cikin sauran qarfin jikin sa da lafiya ga kuma guzuri.

Aikin ya na da marmari ga wanda bai taɓa zuwa ba har kuma ta kan kai wasu gajiya a tsakiyar aikin musamman don tsawon tafiya da kafa. Tun a na murmushi har a fara nishi sama-sama ƙarshe a samu waje a zauna. Sai ka ga duk marmarin nan da zarar an idar da aikin sai wasu su matsa lamba sai sun dawo gida har ta kai ga yin zanga-zanga da furta baƙaƙen kalamai.

A ƙarshe bayan dawowa gida da wasu ‘yan watanni sai ka ga masu irin wannan ɗabi’a na sha’awar sake samun damar komawa. Wannan na daga babbar darajar da Allah ya yi wa ƙasa mai tsarki.

Duk Musulmi na kwarai na addu’ar Allah ya hore ma sa damar gudanar da wannan aiki mai daraja. Wasu ƙasashe da ke kusa da Saudiyya irin Sudan kan ratsa ta Bahar Maliya ne su shiga don aikin hajji.

Mutan Yaman kan shiga mota su shigo Saudiyya don aikin. Ƙasashe masu nisa ke buqatar jirgin sama don samun sauƙin wannan muhimmiyar tafiya.

Bisa yadda canjin dala ke hawa da sauka, hukumar alhazan Nijeriya ta ce duk wanda zai biya kujera yanzu zai ba da daga Naira 8, 254, 464 a arewa sai Naira miliyan 8, 454, 464 a kudu.

Hakanan hukumar ta sanar da rufe karvar kuɗi ranar alhamis 28 ga watan jiya na Maris indai ba wani dalili ya sa an samu karin lokaci ba.

Hukumar alhazan ta ce wannan bai shafi mutum 50,000 da su ka riga su ka biya kuɗin kujerar Naira miliyan 4.9 kafin wannan kari amma su ma duk da samun tallafin gwamnati za su cikato Naira miliyan 1.9.

Fatima Sanda Usara ce mataimakiyar daraktar labaru ta hukumar “mutum 50,000 da tuni su ka biya kuɗin kujera za su yi ciko ne don sun samu tallafin gwamnati da rage-rage da hukumar ta samar. Zuwa alhamis ɗin nan da ƙarfe 12 na dare za mu rufe karvar dukkan kuɗi don gargaɗin da hukumomin Saudiyya su ka yi ma na kan jinkirin.”

A nan hukumar ta ce duk wanda ke son amsar kuɗin sa zai iya rubutawa hukumarsa ta jihar su don a biya shi.

Majalisar ƙoli ta shari’ar Musulunci ta buƙaci gwamnatin tarayya da gwamnoni su tallafa wajen yi wa maniyyata cikaton kuɗin.

Malam Nafi’u Baba Ahmed shi ne babban sakataren majalisar “Zai yi wuya a iya gudanar da akin hajjin ba tare da tallafin gwamnati ba. Mu na ba da shawarar gwamnatoci su tallafawa maniyatan a aikin hajjin bana in ya so baɗi in Allah ya kai mu sai a sake sabon lale. “

Alqaluman hukumar sun nuna zuwa yanzu jihar Kaduna ke da mafi yawan maniyyata 4,656 yayin da Kogi da Ebonyi ke da mafi ƙaranci mutum 13 kowacce Inda Abia, Akwa Ibom, Anambra da Kuros Ribas ba su da ko mutum ɗaya.

Hukumar alhazan Nijeriya NAHCON ta qara fitowa da jan hankalin maniyyata aikin hajjin bana su yi takatsantsan da ‘yan damfara da kan yi amfani da duk wata dama don cutar maniyyatan.

Jami’ar labarun hukumar Fatima Sanda Usara ta fitar da sanarwa dauke da wata lambar wayar kamfanin MTN da nuna a yi hankali da duk bayanai daga lambar.

Lambar 07065319181 dai kamar yanda hukumar ke ankarar da maniyyatan ta ‘yan damfara ce kuma duk bayanai daga lambar ƙarya ne.

NAHCON ta ce ta na amfani da hanyoyin ta da ta saba a hukumance don fitar da sanarwa.

Ba mamaki don yanayin dan karen tsadar kujerar hajji a bana ya sa miyagun iri ke amfani da damar wajen nuna wasu hanyoyin sauƙi don damfarar masu niyyar zuwa sauke faralin.

Ƙalubalen ba ya shafi aikin hajjin bana kaɗai ba ne hatta masu niyyar umrah a cikin azumin nan da ke bankwana. Hukumar alhazan Nijeriya NAHCON ta ce ta na ɗaukar matakai wajen neman maslahar cijewar samun VISA ga masu niyyar tafiya Umrah a azumin nan.

Ofishin jakadancin Saudiyya ya tsayar da ba da VISA don yanda wasu ‘yan Nijeriya su ka zauna a Saudiyya ta amfani da VISA mai tsawon wata 3 da su ka samu.

Kazalika wasu sun samu VISAR mai tsawo amma sai su ka ki tafiya sai a Ramadan ɗin.

NAHCON ta ce ta na tuntubar hukumomin Saudiyya don warware damuwar.

Sanarwa daga mataimakiyar daraktar labaru ta hukumar Fatima Sanda ta ce lokaci-lokaci VISA kan fito idan wani ya dawo daga Saudi ya ba da fagen rage yawan mutane.

A nan sanarwar ta shawarci masu niyyar su yi takatsantsan da irin wannan dama don a kan iya samun cikas.

A yanzu haka a na jiran sanarwa daga hukumar alhazan Nijeriya NAHCON kan adadin maniyyatan da su ka cika kuɗin kujerar aikin hajjin bana.

In za a tuna tun a ƙarshen watan jiya wa’adin biyan cikon Naira miliyan 1.9 ga mutum 50,000 da tun farko su ka biya Naira miliyan 4.9 ya cika.

Kazalika sai kuma yiwuwar samun sabbin waɗanda su ka biya kujerar gaba ɗaya da babu tallafi a ciki.

Masu ruwa da tsaki sun yi ta kira kan gwamnatoci su ƙara tallafawa maniyyatan.

Haƙiƙa lokacin tura kudin waɗanda za su samu shiga jerin aikin hajji ga Saudiyya ya na ƙara ƙurewa ainun.

Kammalawa;

Labarin wasu jihohi sun cikawa maniyyatan su wani kaso daga kuɗin kujerar hajji abun farin ciki ne. Shawara ga duk wanda kuɗin sa ba su cika ba ya haƙura har lokacin da Allah ya hukunta zai tafi wannan gagarumar ibada.

Kyautata niyya da sanin wannan aikin ibada ne bisa dokokin addini na da muhimmanci. Ko Naira miliyan nawa kujerar ta kai matuƙar Allah ya kira mai niyya to zai je cikin aminci.