Da Ɗumi-ɗumi: Ɗan shekara 38 ya zama sabon Mataimakin Gwamnan Edo

Daga BASHIR ISAH

An naɗa matashi ɗan shekara 38, Omobayo Marvellous Godwins, a matsayin sabon Matakin Gwamnan Jihar Edo.

Naɗin nasa ya biyo bayan tsige Mataimakin Gwamnan mai barin gado, Philip Shaibu da Majalisar Dokokin Jihar ta yi ne.

Omobayo injiniya ne a fannin lantarki kuma ɗan asalin ƙaramar hukumar Akoko-Edo da ke jihar.

An tsige Shaibu a muƙamin mataimakin gwamnan jihar ne yayin zaman da majalisar ta yi a ranar Litinin.

Majalisar ta ɗauki matakin tsige Shaibu ne bisa shawarwarin Kwamitin Binciken da ya gudana ƙarƙashin Justice S.A. Omonua-led mai murabus, binciken da aka gudanar bayan da Majalisar jihar ta zargi Shaibu da bayyanar da sirrin gwamnatin jihar.

Rahoton kwamitin ya nuna cewa, an samu ƙwararan hujjoji kan cewa wanda ake zargi ya aikata laifin da ake zarginsa da aikatawa.