Yanzu-yanzu: Shaibu ya yi watsi da tsige shi da aka yi a muƙamin Mataimakin Gwamnan Edo

Daga BASHIR ISAH

Tsigaggen Mataimakin Gwamnan Jihar Edo, Philip Shaibu, ya yi watsi da matakin da Majalisar Dokokin Jihar ta ɗauka na tsige shi a matsayin mataimakin gwamnan jihar.

Shaibu ya bayyana haka ne cikin wani faifan bidiyon da ya wallafa a shafinsa na X jim kaɗan bayan da majalisar jihar ta sige shi.

A ranar Litinin Majalisar Dokokin Jihar Edo ta tsige Shaibu daga muƙamin nasa bayan da ta karɓi rahoto kan binciken da aka gudanar a kansa, kana ta maye gurbinsa matashi ɗan shekara 38, Omobayo Marvellous Godwins, a matsayin sabon Matakin Gwamnan Jihar Edo.

Majalisar ta kafa kwamitin bincike ƙarƙashin Justice S.A. Omonua-led mai murabus, don ya binciki Shaibu kan zargin da majalisar take yi masa na bayyanar da sirrin gwamnatin jihar.

Majalisar ta ɗauki matakin tsige Shaibu ne bisa shawarwarin Kwamitin Binciken da ya gudana ƙarƙashin Justice S.A. Omonua-led mai murabus, binciken da aka gudanar bayan da Majalisar jihar ta zargi Shaibu da bayyanar da sirrin gwamnatin jihar.

Rahoton kwamitin ya nuna cewa, an samu ƙwararan hujjoji kan cewa wanda ake zargi ya aikata laifin da ake zarginsa da aikatawa.