Da Ɗumi-ɗumi: Laraba Saudiyya za ta yi Ƙaramar Sallah

Daga BASHIR ISAH

Ƙasar Saudiyya ta bayyana cewa, ya zuwa ranar Laraba, 10 ga watan Afrilun 2024 za a yi Ƙaramar Sallah a ƙasar.

Ta ce hakan ya faru ne sakamakon rashin ganin jinjirin watan Shawwal a ranar Litinin wanda hakan ya sa za a yi azumin Ramadan 30 a ƙasar.

Kafin wannan lokaci, masana da masu bincike a fagen ilimin taurari sun ce da wahala a ga jinjirin watan Shawwal a ranar Litinin saboda yanayin tafiyar duniyar wata da ta rana.

Da wannan, ya tabbata Laraba ce 1 ga watan Shawwal, 1445AH a ƙasar Saudiyya.