Bikin Sallah: Duk gidan wasan da ya aikata ba daidai ba a Kano zai rasa lasisinsa — El-Mustapha

Daga RABIU SANUSI

A ƙoƙarin sa na tabbatar da ana bin dokoki sau da ƙafa, Shugaban Hukumar tace fina-finai da ɗab’i ta jihar Kano. Abba El-mustapha, ya kafa wani kwamiti na musamman wanda zai lura da yadda gidajen wasanni a Kano zasu gudanar da shagul-gulan bikin ƙaramar sallah.

El-mustapha ya wannan jawabin ne a ranar Litinin yayin ƙaddamar da shugabancin kwamitin da mambobinsa, ƙarƙashin jagoranci daraktan kuɗi da mulki na Hukumar, Alh. Abdulkarim Badamasi, sai darakta mai lura da sashin shirya fina-finai, Alh. Idiris Zakari Ya’u Zaura.

Sauran sun haɗa da Daraktan kula da sashen ɗab’i, Alh Abubakar Zakari Garin Babba, sai masu aika wa gwamna rahoto na musamman da ya shafi Hukumar, wato (SSR da SR) da kuma sauran ma’aikatan Hukumar a matsayin mmmbobin kwamitin.

El-mustapha ya ce manufar kafa wannan kwamitin shi ne, tabbatar da bin doka tare da daƙile duk wani abu da ake tunanin zai ci karo da al’ada ko tarbiyyar addinin Musulunci.

Haka nan, ya ce aikin kwamitin shi ne, zagayawa gidajen wasannin domin lura da su tare da kawo wa Hukumar rahoto kan yadda suka gudanar da shagul-gulan bikin sallar, a inda ya kuma yi kira ga waɗanda aka zaɓo a matsayin ‘yan kwamitin da su maida hankali a kan aikin da aka ɗora su.

Abba ya sha alwashin hukunta duk wani gidan wasan da aka samu da laifin karya doka wanda hukuncin ka iya kaiwa ga ƙwace lasisin sa na din-din.

A ƙarshe, ya kuma yi kira ga masu gidajen wasannin dake faɗin Jihar Kano musamman masu gidajen gala da sauran gidajen kallon dake gudanar da wasa a lokacin bikin sallah da su bi dokar Hukumar sau da ƙafa kamar yadda suka saba yi a baya.