Da Ɗumi-ɗumi: Ba a ga watan Ƙaramar Sallah ba a Nijeriya — Sarkin Musulmi

Daga BASHIR ISAH

Sarkin Musulmi, Alh Abubakar Sa’ad, ya tabbatar da cewa ba a jinjirin watan Shawwal ba a Nijeriy a wannan Litinin ɗin.

Don haka ya buƙaci al’ummar Musulmi ƙasar su cika azumi watan Ramadan zuwa 30, ta yadda ya zuwa Laraba, 10 ga Afriluu 2024, sai a yi bikin Ƙaramar Sallah.

Da wannan, ya tabbata cewa Laraba ce 1 ga watan Shawwal, 1445AH.

Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labarai da Kwamitin bai wa Sarkin Musulmi Shawar kan lamurran addini ya fitar ranar Litinin mai ɗauke da sa hannun Fargesa Sambo Wali Junaidu, wanda shi ne shugaban kwamitin.

Wannan na zuwa ne bayan da ƙasar Saudiyya ta ba da sanarwa rashin ganin jinjirin watan Shawwal a ƙasar.