An ga watan Ƙaramar Sallah a Nijar

Daga BASHIR ISAH

Hukumomi a Jamhuriyar Nijar sun ce an ga watan Ƙaramar Sallah a wasu jihohi biyar na ƙasar.

Don haka, Talata take 1 ga Shawwal kuma ranar Ƙaramar Sallah a ƙasar.

Sai dai, maƙwabciyar Nijar, wato Nijeriya da Saudiyya da sauransu, aun ce ba su ga wata ba, wanda hakan ya sa za su yi azumi 30 a ƙasashen sannan Laraba su yi Ƙaramar Sallah.