Bikin Sallah: KAROTA ta gargaɗi ma su ganganci da abin hawa

Daga RABI’U SANUSI a Kano

Hukumar Kula da Zirga-zirgar Abubuwan Hawa ta Jihar Kano (KAROTA), ta haramta guje-guje da ababen hawa a lokutan bikin Ƙaramar Sallah a faɗin Jihar.

Hukumar ta sanar da hakan ne ta cikin wata sanarwa da Kakakinta, Nabilusi Abubakar Kofar Na’isa, ya aiko wa MANHAJA a ranar Litinin, inda ya ce sun ɗauki matakin ne a sakamakon yadda guje-guje da ababen hawa ke zama barazana ga rayuwar al’umma.

“Hakan ne ya sa hukumar ta ce za ta girke jami’anta guda 1500 domin sa ido a shagulgulan bikin Sallah a lungu da saƙo na jihar, domin su tabbatar da jama’a sun kiyaye dokokin tuƙi.

Haka kuma, Hukumar ta ja hankalin iyaye da su guji bai wa yaran da suke ƙasa da shekara 18 abin hawa domin tuƙawa, tana mai cewa ba za ta lamunci wannan ɗabi’a ba.

Kazalika, ta ja hankalin jama’a da su kiyaye tare da bin doka sau da ƙafa, domin guje wa haɗurra a lokacin shagulgulan bikin Sallah.

Inda a ƙarshe ta yi fatan alkhairi ga jama’a tare da fatan za a shagulgulan bikin Sallah cikin kwanciyar hanlaki da lumana.