Azumi da iyalanmu

Daga AISHA ASAS

A cikin littafi mai tsarki, Allah Mai Girma da Ɗaukaka Ya sanar da mu daraja da falalar da ke cikin watan Ramadan, daga ciki kuwa har da ‘yanta bayi daga shiga wuta, samun dace da dare mafi daraja da ke cikin watan, daren da ya fi darare dubu a nauyin lada, wato daren Lailatul Ƙadar.

Da yawa daga cikinmu idan an ambaci watan Ramadan hankalinmu da tunaninmu zai karkata ne ga iya yawaita ibada, karatun Alƙur’ani, yawan sallah da kame kai daga zina.

Wanda hakan ya ɗauke tunaninsu daga kallon kyautatawa iyali a matsayin ɗaya daga cikin kyawawan da za su iya sada ka da dacewa a cikin wannan wata.

Don haka ne shafin Iyali na wannan mako zai yi tsokaci kan muhimmancin kyautatawa iyali a cikin watan Ramadan da kuma hanyoyin da ya kamata a bi don samar da ƙarin kyautatawa a zamantakewa.

Anan idan na ce kyautatawa iyali ba na tsaya a iya maigida ba ne, sai dai zan soma ne kansa a matsayin sa na babba a gida.

Manzon rahma ya ce, “Mafi alkhairi daga cikinku shi ne mai kyautatawa iyalansa. Kuma ni ne (shi Manzon Allah) mafi alkhairi daga cikinku.”

Idan mun ɗauki wannan faɗa ta ma’aiki, za mu fahimci cewa, kyautatawa iyali abu ne mai matuƙar muhimmanci, ba wai a iya lokacin Ramadan ba, domin ya bayyana yadda yake kyautatawa iyalinsa ta hanyar kiran kansa mafi alkhairi, wato yana matuƙar kyautata masu.

Kamar yadda ƙissoshi da dama tare da hadisai suka yi bayani, Manzon Tsira kan taimakawa matansa da aikace-aikace na gida, yakan yi masu uziri idan suka yi wauta irin na mata, kuma yana ririta su wanda ke nuna matuƙar muhimmanci da suke da shi.

Duk waɗannan kyautatawa ce, kuma ba ka kasance mijin Hajiya ba don ka aikata hakan ga matanka, don kaga fiyayyen halitta ma ya yi, wanda ya fi ka, ya fi duk wata halitta da ke yawo a doron ƙasa.

Idan mun koma kan darasin namu, an so a watan Ramadan duk wata kyautatawar da ka ke yi wa iyalanka ka ninka idan watan ya shigo.

Ba wai na iya abin ci da sha ba, wannan shi ne gaba, domin babu albarka ga dukiyar wanda ke matsar da iyalinshi a cikin wata mai tsarki.

An so idan kana da zarafi su sabunta, ka ba su mafifici daga abinda ka saba ba su idan kana da zarafin yin hakan.

Baya ga wannan, kyautatawa ba ta tsaya iya nan ba, domin ko tausasa murya yayin magana da matarka aiki ne na lada babba, kuma zai iya zama ɗaya daga cikin manya daga ababen da za su iya cika ma’unin ibadarka ta watan Ramadan.

Gode wa ƙoƙarin da matarka ke yi na daga kula da gida, dafa abinci zuwa tabbatar da kowa ma ya samu abincin da zai sha ruwa da shi kafin buɗa-baki shi ma sadaka ne.

Kawar da kai daga kuskurenta ko gazawarta a watan shi ma wata hanya ce da ya kamata ka bi don neman yardar ubangiji a wata irin wannan.

Idan na koma kanki uwargida, ki sani, ba ki buƙatar yawon zuwa sallar tahajud ko assham alhali mijinki bai kuɓuta daga tozartawa daga gare ki ba.

Kada ki tsammaci rahmar Allah alhalin kowanne buɗa-baki da baƙin cikinki mijinki ke fara shan ruwa da shi.

Idan har ba ki gode wa ƙoƙarin sa ba, ko ba ki yi haƙuri da gazawarsa wadda ki ka sani babu ce ta janyo hakan ba, ban san ta yadda za ki kalli ubangiji ki ce Ya gafarta miki ba.

Annabin rahma ya ce, “Da zan umurci wani mutum ya yi wa wani sujjada, da na umurci mata ta yi wa mijinta sujjada.”

Idan kin fahimci wannan hadisin da kyau, za ki gane ba wata hanyar da za ki iya samun shiga layin waɗanda za su samu rabauta a wata mai tsarki alhali kina cutattar da mijinki.

Koda kuwa za ki kwana salla, kina wahalar da kanki ne matuqar ba ki shimfiɗa gaskiya a zamantakewar ki da mijinki ba.

Ba wai na ce idan mijinki na fushi da ke ba kawai, koda ba ya fushi da ke, mutuƙar kina cutar da shi.

Ko yana fushi da ke, matuqar ba cutar da shi ki ka yi ba, ba ki cikin layin da nake magana kansu.

Ya ku ‘yan uwa Musulmai, mu daure mu gyara alaƙarmu da iyalanmu a cikin watan Ramadan, mu kyautata masu matuƙar kyautatawa, sannan mu guji cutar da su, matuƙar muna son mu kasance cikin ‘yantattun bayin Allah.

Allah Ya karɓa daga gare ni, da gare ku.