Abin da Shugaban NFC, Ali Nuhu suka tattauna da Jakadan Spaniya a Nijeriya

Daga BASHIR ISAH

A ranar Litinin ta wannan makon Shugaban Hukumar Shirya Fina-finai ta Ƙasa (NFC), Dokta Ali Nuhu, ya yi ganawa ta musamman a Abuja tare da Jakadan Ƙasar Spaniya a Nijeriya, Juan Ignscio Sell, inda suka tattauna kan muhimman batutuwa.

Tattaunawar tasu ta shafi samar da ƙawance tsakanin NFC da Spaniya domin bunƙasa harkokin masana’antar ƙirƙire-ƙirƙire a Nijeriya.

Da yake jawabi, Ali Nuhu ya yaba wa Jakada Sell bisa goyon bayan da ofishinsa kan bai wa masana’antar, tare da neman ya faɗaɗa goyon bayan nasa zuwa ga hukumar NFC don bunƙasa harkar shirya fina-finai da sauransu a Nijeriya.

A nasa ɓangaren, Jakadan ya ce ƙasarsa Spaniya ta jaddada aniyarta ta mara wa bikin baje kolin fina-finai, wato Zuma Film Festival – 2024, tare da cewar ƙasar za ta shiga bikin dumu-dumu.

Bikin na bana zai taɓo ɓangarori da dama, da suka haɗa da samun ƙawance tsakanin Nijeriya da Spaniya, horaswa da musayar shirye-shirye da dai sauransu.

Tun bayan da Shugaba Tinubu ya naɗa shi a matsayin Shugaban Hukumar Fina-finai ta Ƙasa (NFC), Ali Nuhu ya yunƙura domin ba da tasa gudunmawa ga cigaban masana’antar shirya fina-finai a Nijeriya.