Gwamnatin Nijeriya ta ƙara hutun Ƙaramar Sallah

Daga BASHIR ISAH

Gwamnatin Tarayyar Najeriya ƙarƙashin jagorancin Shugaba Bola Tinubu, ta amince da ranar Alhamis, 11 ga watan Afrilu, 2024, a matsayin ƙarin hutun aiki domin bukukuwn Ƙaramar Sallah.

Bayanin haka na ƙunshe a cikin wata sanarwa da Ministan harkokin cikin gida, Olubunmi Tunji Ojo ya fitar a madadin Gwamnatin Tarayya.

Da fari, rakunan Talata da Laraba na wannan makon Gwamnatin ta ayyana a matsayin ranakun hutu don bikin salla, amma daga bisani ta ƙara zuwa Alhamis sakamon Ƙaramar Sallah ta faɗa Laraba.

Ministan ya yi amfani da wannan dama wajen taya al’ummar musulmi murnar kammala wata guda na gudanar da ibadar azumi, ya kuma nanata ƙudurin Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu na samar da zaman lafiya da wadata ga ‘yan ƙasa baki ɗaya.