Da Ɗumi-ɗumi: Jaruma a Kannywood, Saratu Giɗaɗo ta riga mu gidan gaskiya

Daga BASHIR ISAH da RABI’U SANUSI

Allah Ya yi wa fitacciyar jaruma a masana’antar shirya fina-finai ta Kannywood, Saratu Giɗaɗo wadda aka di sani da Daso, rasuwa.

Jarumar ta rasu ne a ranar Talata kamar yadda wani makusancinta ya bayyanawa MANHAJA.

Da yake amsa tambayar wakilinmu, makusancin marigayiyar ya ce lafiya ƙalau Saratu ta wayi gari a wannan rana.

Ya ƙara da cewa, hasali ma Mmarigayiyar ta ɗauki azumi a wannan rana.

Har wa yau, wata majiyar ta sheda ma wakilinmu cewa, “Saratu Gidado tana fama da rashin lafiya a tsaitsaye ne, wanda a yau kuma ta yi mutuwar Fuj’a”.

Daga yanzu zuwa kowane lokaci, za a sanar da lokacin da za yi wa marigayiyar jana’iza daidai da karantarwar addinin Musulunci.

Kawo yanzu, masoyan jarumar daga sassa daban-daban daban na vi gaba da nuna kaɗuwarsu game da mutuwar tata.