Gwamnan Kano ya sake naɗa Ogan Ɓoye kan muƙaminsa

Daga IBRAHIM HAMISU a Kano

Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusif, ya sake bai wa Yusuf Shuaibu Imam (Ogan Boye) muƙamin da ya ƙwace na mai ba shi shawara na musamman kan harkokin matasa da wasanni.

Abba ya sake naɗa Ogan Ɓoyen a karo na biyu ne a cikin wasu sabbin naɗe-naɗe da ya yi a daren da ya gabata, kamar yadda sanarwar Babban Daraktan Yaɗa Labaransa, Sanusi Bature Dawakin Tofa ta tabbatar.

Daga cikin sabbin naɗe-naden da Gwamnan ya yi sun haɗa da:

Farfesa Ibrahim Magaji Barde, mai ba da shawara na musamman kan harkokin tattara kuɗaɗen shiga (IGR);
Dakta Abdulhamid Danladi, mai ba da shawara na musamman na biyu kan harkokin ‘yan Kano mazauna ƙasashen waje.

Sai kuma Injiniya Bello Muhammad Kiru, mai ba da shawara na musamman kan albarkatun ruwa;
Yusuf Shuaibu Imam (Ogan Boye), an sake naɗa shi a matsayin mai ba da shawara na musamman kan harkokin matasa da wasanni; Dakta Nura Jafar Shanono an canza masa muƙami daga mai ba da shawara na musamman kan albarkatun ruwa zuwa Manajan Daraktan hukumar samar da ruwan sha ta jihar Kano (WRECA).

Haka kuma, shi ma Honarabul Baba Abubakar Umar an canza masa muƙami daga mai ba da shawara na musamman zuwa Babban Sakataren Gudanarwa na Hukumar Kula da Makarantu Masu Zaman Kansu da na sa kai.

Sai kuma Honarabul Nasir Mansur Muhammad wanda aka naɗa shi Darakta Janar, mai kula da Ƙanana da amatsakaitan Masana’antu (SMEs); Aminu Hamidu Bako Ƙofar Na’isa zai zama mataimakin Manajan Darakta (DMD), Hukumar Noma da Raya Karkara ta Kano (KNARDA).

Sai kuma Injiniya Mukhtar Yusuf, Mataimakin Manajan Darakta (DMD), a Hukumar Samar da Ruwan Sha ta Jihar Kano (WRECA).

Sanarwar ta ƙara da cewa, duka naɗe-naɗen sun fara aiki ne nan take.

Idan za a iya tunawa tun a ranar 15 ga watan Satumban 2023 Gwamnan Kano ya kori Ogan Ɓoye daga kan muƙaminsa, bayan da ya zarge shi da furta kalaman da ba su dace ba a madadin gwamnatinsa.