Masu harkar DJ sun koka kan haramta musu sana’a a Katsina

Daga UMAR GARBA a Katsina

Ƙungiyar masu kiɗan DJ reshen jihar Katsina, ta koka dangane da hana sana’ar a faɗin jihar.

Shugaban ƙungiyar a jihar, Hassan Mamman, ya bayyana irin halin da mambobin ƙungiyar za su shiga bayan da hukumar Hisba ta jihar Katsina ta hana gudanar da sana’ar.

Ƙungiyar ta bayyana damuwwarta a wani taro da ta kira don wayar wa al’umma da kuma hukumar Hisba ta jihar kai game da yadda mambobinta suke tafiyar da sana’ar DJ a jihar.

A cewar shugaban ƙungiyar sun ɗauki harkar DJ a matsayin sana’a, ba suna yi ba ne don ɓata tarbiyyar al’umma ko kuma tara mata da maza a wuri ɗaya don aikata baɗala.

A cewarsa, da sana’ar suke ciyar da iyalansu, ba su iya wata sana’a bayan DJ, daga nan ya bayyana irin gudummawa da ƙungiyar ta ba wa gwamnan jihar gudunma matuƙa lokacin da yake nema zama gwamnan jihar Katsina.

Saboda haka ƙungiyar ta roƙi gwamnatin jihar da sauran al’umma a kan su sake duba lamarin duba da irin yanayin matsin rayuwa da za su shiga bayan an raba mambobinta da sana’arsu.

Idan za a iya tunawa MANHAJA ta rawaito cewar, hukumar Hisba a jihar ƙarƙashin jagorancin Babban Kwamandanta, Malam Aminu Usman (Abu Ammar) ta haramta gudanar da wasu ayyukan ɓata tarbiyyar al’umma da suka haɗa da: Ayyukan Kiɗe-kiɗe na DJ da harkar Sara Suka (ƙauraye) da Wasan Gala da kuma shirya tarurrukan bukukuwan aure da suka saɓa wa shari’a.