Sani Muazu ya nuna kaɗuwarsa kan rasuwar Daso

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Kwamitin Amintattu na Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Masu Shirya Finafinai ta Nijeriya (MOPPAN), Sani Muazu, ya bayyana alhini da kaɗuwarsa dangane da rasuwar jarumar Kannywood, Saratu Giɗaɗo wadda aka fi sani da Daso.

Ya bayyana haka ne cikin bayanin da ya fitar dangane da rasuwar marigayiyar a ranar Talata.

Ya ce, “Cike da alhini na bi sahun ‘yan uwa wajen sanar da rasuwar ɗaya daga cikin fitattun jaruman Kannywood, Hajiya Saratu Giɗaɗo, wacce masoyanta suka fi kira da Daso.

“Rasuwarta ta zo da kaɗuwa saboda ƙalau take ba ta fama da wani rashin lafiya. Cikin ƙoshin lafiya ta kwanta a daren jiya kamar yadda babban ɗanta ya tabbatar, sai ga shi a yau ta kwanta dama.

“A cikin barci ta rasu. Lamarin akwai kaɗuwa ainun, amma a matsayin Muslmi, mun san cewa mutuwa aba ce wadda babu makawa sai an ɗanɗane ta kuma tana iya zuwa a kowane lokaci. Inna lillahi wa ınna ilaihir rajiun,” in ji shi.

Ya ƙara da cewa, ba za a mance da marigayiyar ba saboda irin rawar da ta taka a indostiri inda takan hau kowane irin matsayi da aka ɗora ta a fim yadda kamata.

Kazalika, Sani ya ce marigayiyar ta shafe aƙalla shekara 20 a masana’antar shirya finafinai: “Ni kaina mun yi aiki tare a finafinai da dama. Har zama ta yi da iyalina a Jos a lokacin da ake aikin ɗaukar fim ɗin ‘Dan-Gari’ wanda na ba da umarni.

“A madadin iyalina da Kwamitin Amintattu na MOPPAN, ina miƙa ta’aziyya ga ahalin marigayiyar da ɗaukacin abokan aiki da ke Kano haɗi da kafatanin masa’antar shirya finafinai a Nijeriya bisa wannan babban rashi da ya same mu. Da fatan Allah SWT ba mu hakiri da juriyar wannan rashi,” in ji Sani.