Ƙaramar Sallah: Gwamnan Zamfara ya miƙa saƙon goron sallah ga al’ummar Musulmi

*Ya buƙaci a yi wa ƙasa addu’ar zaman lafiya

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Dauda Lawal na Jihar Zamfara, ya taya al’ummar Musulmi murnar bikin Ƙaramar Sallah, tare da kira kan yi wa Zamfara da ma ƙasa baki ɗaya addu’ar samun dauwamammen zaman lafiya.

Lawal ya miƙa saƙon nasa ne cikin sanarwar da Kakakinsa, Sulaiman Bala Idris, ya fitar.

Sanarwar ta ce watan Ramadan da ya ƙare ya bai wa ‘yan ƙasa damar zazzaga wa ƙasa addu’o’in samun zaman lafiya da kuma kwaranyewar matsalolin tsaron da ƙasa ke fama da su.

Ta ƙara da cewa, yana da kyau Musulmi su ci gaba da ɗabbaƙa darussann da suka koya a Ramadan a sauran lokuta.

“Eid al-Fitr lokaci ne na farun ciki wanda ke nuni da kammaluwar azumin watan Ramadan.

“A rabar Idi, Musulmi kan nuna godiya bisa lafiya da kuma damar da Allah Ya ba su wajen sauke faralin azumin Ramadan.

“Mu yi amfani da wannan lokaci wajen wanzar da zaman lafiya da lumana.

“Domin magance matsalolin tsaron ƙasa, dole mu zamo masu lura da junanmu da kuma dakewa kan yi wa ƙasa addu’a tare da mara wa ƙoƙarin gwamnati baya wajen kakkaɓe manyan laifuka a cikin al’umma.

“Ina taya Musulmin Zamfara da na Nijeriya da ma duniya baki ɗaya murnar wannan biki, da fatan Allah Shi maimaita mana cikin ƙoshin lafiya,” in ji Gwamna Lawal.