Na samu rufin asiri a sana’ar rubuta finafinai – Yahaya S. Kaya

Daga IBRAHIM HAMISU, a Kano

Yahaya S. Kaya fasihin marubucin labarin fim ne, da ya rubuta finafinai fiye da 20 a masana’antar fim ta Kannywood. A tattaunawasa da Ibrahim Hamisu a Kano za ku ji cikakken tarihinsa da kuma irin nasarorin da ya samu cikin shekaru 8 da shigar sa Kannywood, ku biyo mu:

MANHAJA: Ka gabatar mana da kanka?

YAHAYA S. KAYA: Sunana Yahaya S Kaya. Ni marubuci ne, ina rubutun littafi, ina na film.

Ko za ka ba mu taƙaitaccen tarihinka?

An haife ni a Garin Zariya, a shekarar 1996, na ta so a garin Zariya, anan na yi karatu na har zuwa matakin National Diploma, na karanci ‘Computer Science’, yanzu ina ɗaura ‘degree’ na ‘online’ a wata makaranta University Of The People da ke Ƙasar California.

Me ya baka sha’awa ka shiga masana’antar Kannywood?

Ni ba ma’aboci karatun littafan Hausa ba ne, watarana ina makaranta, sai na ga wani abokina da wani littafi ‘Mata Hudu’, na ce ya aramun na karanta, ya bani tunda na karanta na ji a raina kamar zan iya rubutu, sai na fara gwada rubuta wani littafi ‘Ɗan Shugaban Ƙasa’, wannan shi ne sanadin fara rubutuna.

Fim yana da ma’aikata da yawa kai a wane bangare ka fi ƙwarewa?

Nafi ƙwarewa a rubutun fim, ma’ana ni marubuci ne.

A wacce shekara ka fara fim, kuma da wane fim ka fara?

Na fara rubutun fim a shekarar 2016, film ɗina na farko da na rubuta aka fara fim ɗinsa sunan shi ‘Ruhin Safna’.

Ya zuwa yanzu finafinai nawa ka rubuta?

Gaskiya na rubuta finafinai sun fi 20. Wasu a ciki ni kaɗai na rubuta, wasu kuma haɗaka ne da sauran marubuta. Wasu daga cikin sun haɗa da; ‘Dafin Zuciya’, ‘Zuciya’, ‘Sirrin Ɓoye’, ‘Ke Duniya’, ‘Alhaki’, ‘Agolan Ƙauye’.

Baya ga rubutawa a wane ɓangare ka ke son ƙwarewa?

Ina so na fara shirya fim ɗina na kaina, idan Allah ya ara min lokaci.

Daga lokacin da ka fara zuwa yanzu waɗanne irin nasarori za ka iya cewa ka samu?

Uhmm, alhamdulillah, gaskiya kam ba ƙarya, na samu nasarori ta kowacce fuska, babu nasarar da tafi ka kasance cikin rufin asiri, na samu rufin asiri da sana’ar rubutu, na ƙara ƙima sosai a idon mutane, har da wanda ba su sanni ba idan aka ce musu ni marubuci ne, suna girmama hakan.

Wane irin ƙalubale za ka iya cewa ka samu ?

Ba zance bana fuskantar ƙalubale ba, amma ga duk wanda ya san mecece rayuwa dole ya tsammaci zuwan ƙalubale, idan ma nasara ta zo maka babu ƙalubale a tattare da ita ya kamata ka ƙalubalanci kanka.

Wane ne maigidanka a Kannywood?

Bani da maigida a Kannywood, amma ina da mutanen da nake ɗaukar su a matsayin masu gidana, wanda ba zan iya tsallake ma maganarsu ba, saboda ƙima da girmansu da nake gani.

Ko zaka iya tuna wani fim da ya baka wahala wajen rubuta shi?

Labarin da ya bani wahala, shi ne fim ɗin ‘Yahoo Boy’, saboda akwai bincike sosai, idan ka lura da yanayin fim ɗin ba Bahaushen Labari ba ne.

A cikin finafinan da ka rubuta wane ka fi so?

Duk finafinan da na rubuta Ina son su, amma film cun ‘Agolan Ƙauye’, saboda ‘comedy’ ne, wato na barkwanci ne, kuma ya bani wahala, kasancewa shi ne ‘comedy’ na na farko, Ina son shi sosai.

Salon wane marubuci ka ke amfani da shi?

Salon marubuci Yahaya S Kaya. Ni ne ‘role model’ xin kaina (murmushi).

Menene burinka a nan gaba?

Burina ya zamana na tafi na bar tambari mai kyau da ba za a manta da ni ba a masana’antar Kannywood. Sannan ina da burin fara rubuta finafinan Turanci.

Idan kai ne shugaba a Kannywood waɗanne abubuwa ne ka ke ganin ya kamata a gyara?

Idan da ace ni ne shugaba a Kannywood abubuwan da zan yi ƙoƙarin gyarawa, tsayawa tsayin daka wajen ganin an sauke haƙƙin duk wani ma’aikaci da ke masana’antar, samar da doka ta musamman wadda za ta dinga hukunta duk wanda ya ci haƙƙin wani, fito da martaba da ƙimar marubuci, har masu kallo su fahimci shi ma jigo ne babba a cikin fim, ƙoƙari wajen inganta masana’antar tare da samar da kayan aiki, wanda za su motsar da ita gaba.

Wacce shawara za ka bai wa mai shirin shiga Kannywood?

Shawarar da zan ba duk wanda yake so ya shiga Kannywood, su shigo ta tsaftatacciyar hanya, kuma su nemi yardar iyayensu, su saka a ransu sana’a za su yi, su wanke zuciyarsu daga duk wani datti da tunani mara kyau. Saboda ita Kannywood masana’anta ce da take da faɗi, za ka samu duk irin mutanen da ka ke nema.

Mun gode.

Ni ma na gode sosai.