Basarake ya kwanta dama bayan kammala Sallar Idi a Legas

Daga BASHIR ISAH

Allah Ya yi wa Sarkin Masarautar Isolo da ke Jihar Legas, Oba Kabiru Agbabiaka, Adeola Olushi III, rasuwa.

Majiyarmu ta ce basaraken ya rasu ne a ranar Laraba jim kaɗan bayan da ya dawo daga sallar Idi.

Shugaban Yankin Rayawa na Isolo (LCDA), Olasoju Adebayo, ya tabbatar da mutuwar basaraken.

Ya ce za a yi jana’izar marigayin da misalin ƙarfe 4 na yamma daidai da karantarwar Islama.

“Na samu umarnin Gwamman Legas, Mr. Babajide Sanwo-Olu, kan in sanar da rasuwar Sarkin Masarautar Isolo, Oba Kabiru Agbabiaka, Adeola Olushi III, a yau 10 ga Afrilun 2024. Ya rasu yana da shekara 64.

“Za a yi jana’izarsa da misalin ƙarfe 4 na yamma a fadarsa da ke 3/5 Akinbaye Street, Isolo daidai da koyarwar addinin Musulunci,” in ji shi.