Gwamnatinmu za ta ci gaba da cika alƙawurran da ta ɗaukar wa al’umma —Gwamna Abba

  • Ya ce duk wanda zai kawo mana tashin hankali a jihar Kano hukuma za ta yi aiki kansa

Daga RABIU SANUSI a Kano

Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya bayyana ƙudurin gwamnatinsa na cigaba da cika alƙawarin da ya yi wa al’ummarsa yayin neman zaɓe na bambaɗa musu ayyukan more rayuwa.

Gwamna ya bayyana haka ne a ranar Ƙaramar Sallah yayin aike wa al’ummar jihar da ma ƙasa baki ɗaya da saƙon goron sallah.

Ya ce, daga lokacin da gwamnatinsa ta karɓi ragamar mulki zuwa yanzu, sun aiwatar da ayyuka da daman gaske.

Daga nan, ya ƙara jaddada aniyarsa ta ci gaba da yi wa al’ummar Kano ayyukan cigaba da za su ɗaga martabar Kano a matakin ƙasar nan.

Ya bakinsa: “Za kuma mu ƙara yin amfani da wannan damar wajen ci gaba da tabbatar wa da jama’ar Kano cewa gwamnatinmu za ta ƙara ƙaimi wajen kakkaɓe dukkan ɓata-garin da ke yunƙurin kawo mana rashin zaman lafiya.

“Kano gari ne da ke da ɗumbin tarihi na zaman lafiya, amma dan biyan buƙatar wasu daga cikin tsirarun mutane sun addabi jama’a da hana su zaman lafiya.”

Ya ci gaba da shelantawa duniya cewa, batun faɗan daba da wasu ke tunanin za su maido jihar Kano kuwa, su sani gwamnatinsa ba za ta bar su ba, sai mun ɗauki hukuncin da ya dace a kansu.

“Duk wanda ya yi wautar tashin-tashina wajen hana jama’ar Kano zaman lafiya gaskiya hukumar tsaro za su kama shi tare da tasa ƙeyarsa zuwa kotu ɗan ya girbi abin da ya shuka.”

Gwamna Abban ya yi kuma kira ga al’ummar jihar Kano da su ci gaba da sa lura yayin tukin ababen hawa musamman a wannan lokacin bikin ƙaramar Sallah da ake gudanarwa.

Abba Kabir Yusuf ya kuma mika sakon barka da Sallah ga dukkan Al’ummar Musulmai,da fatan anyi sallah lafiya tare da fatan Alkhairi.

Kazalika ya buƙaci jama’ar wannan gari na Kano mai albarka da su ci gaba da tabbatar da nuna dabi’un da suka kowa a cikin wannan wata mai albarka na azumin Ramadhan.

“Muna kira ga al’ummarmu da su ƙara zage dantse wajen yi wa jiharmu addu’a ta neman zaman lafiya da kuma ƙasa baki ɗaya.”

A hannu guda, Gwamna Abba ya yaba wa Shugaban Ƙasa bisa namijin ƙoƙarin sa wajen ɗora wannan ƙasa kan turbar alkhairi.