Ƙaramar Sallah: NSCIA ta miƙa saƙon taya murna ga al’ummar Musulmi

*Ta buƙaci a nemi wata ranar Litinin

Daga BASHIR ISAH

Majalisar Ƙolin Harkokin Musulunci ta Ƙasa (NSCIA), ƙarƙashin jagorancin Sarkin Musulmi, Alh. Muhammad Sa’ad Abubakar, CFR, mni, ta miƙa saƙon taya murna ga al’ummar Musulmin Nijeriya da ma duniya baki ɗaya dangane da bikin Ƙaramar Sallah na bana.

Hakan na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labarai da majalisar ta fitar mai ɗauke da kwanan wata 7 ga Afrilu, 2024 da sa hannun sakataren Majalisar, Farfesa Is-haq Oloyede, CON, FNAL.

Majalisar ta ce, “Muna roƙon Allah Ya maimaita mana mu shaida hakan na shekaru masu yawa kuma cikin ƙoshin lafiya.”

Ta kuma yi amfani da wannan dama wajen nusar da Musulmi muhimmancin Zakkar Kono wanda ta ce “Farali ne a kan duk Musulmin da ke da halin bayarwa zuwa ga miniskinai a cikin al’umma.”

Majalisar ta ƙara da cewa, “Bisa shawarar Kwamitin Duban Wata (NMSC), Shugaban Majalisar na kira ga Musulmin NIjeriya da su nemi jinjirn watan Shawwal  na 1445 A.H. ranar Litinin, 29 ga Ramadan 1445 A.H. wanda ya yi daidai da 8 ga Afrilun 2024, bayan faɗuwar rana.

“Idan Kwamitin ya tabbatar da an ga wata, Sarkin Musulmi zai ayyana Talata, 9 ga Afrilu, 2024 a matsayin 1 ga Shawwal kuma ranar Ƙaramar Sallah.

“Amma idan ya zamana ba a ga wata ba, Ƙaramar Sallah ta faɗa ranar Laraba, 10 ga Afrilu, 2024 ke nan,” in ji sanarwar.

A ƙarshe, Majalisar ta fitar da sunaye da kuma lambobin waɗanda suka cancanta a tuntuva don miƙa saƙon ganin wata kamar haka:

S/NSUNALAMBAR WAYAEMAIL ADDRESS  
1Sheikh Dahiru Bauchi08036121311[email protected]  
2Sheikh Karibullah Kabara08035537382[email protected] 
3Sheikh Habeebullah Adam Abdullahi Al-Ilory08023126335[email protected] 
4Prof. Z. I. Oboh Oseni08033574431[email protected] [email protected] 
5Mal. Simwal Usman Jibrin08033140010[email protected] 
6Sheikh Salihu Yakub07032558231[email protected] 
7Mal. Jafar Abubakar08020878075[email protected] 
8Alh. Abdullahi Umar (Wazirin Gwandu)08037020607[email protected] 
9Prof. J. M. Kaura08067050641[email protected] 
10Dr. Bashir Aliyu Umar08036509363 [email protected] 
11Ustaz Muhammad Rabiu Salahudeen08035740333[email protected] 
12Sheikh Abdur Rasheed Mayaleke08035050804[email protected] 
13Dr. Ganiy I. Agbaje08028327463[email protected] 
14Gafar M. Kuforiji08033545208[email protected] 
15Prof. Usman El-Nafaty08062870892[email protected] 
16Mal. Salihu B.  Zubairu08038522693[email protected] 
17Imam ManuMuhammad08036999841[email protected] 
18Qadee Ahmad Bobboy08035914285[email protected] 
19Ustaz Nurudeen Asunogie08033533012[email protected] 
20Sheikh Bala Lau08037008805[email protected] 
21Sheikh Sani Yahaya Jingir08065687545[email protected] 
22Sheikh AbdurRahman Ahmad08023141752[email protected] 
23Muhammad Yaseen Qamarud-Deen08055322087[email protected] 
24Prof. Sambo Wali Junaidu (Wazirin Sokoto)08037157100[email protected]   
25Sheikh Lukman Imam Abdullahi08052242252[email protected] 
26Sheikh Sulaiman Gumi08033139153[email protected] 
27Alh. AbdulBariu Kareem09096369117[email protected] 
28Prof. Kamil K. Oloso08023098661[email protected] 
29Malam Usman Mahmud08034540120[email protected] 
30Malam Yahaya Boyi (Sarkin Malamai Sokoto)08030413634[email protected] 
31Ustaz Mukail Abdurraheem08099370109[email protected] 
32Ustaz Nurudeen Ibrahim08027091623[email protected]