Dambarwar bashin Kaduna za ta farraƙa El-Rufai da Sani?

Spread the love

*’Ya’yan El-Rufai sun shata daga a junansu

Daga SANI AHMAD GIWA a Abuja

A cikin ’yan kwanakin nan Jihar Kaduna ta ɗau zafi a siyasance kan kukan da gwamnan jihar Malam Uba Sani ya yi kan tulin bashin da ya gada daga tsohuwar gwamnati ta Malam Nasiru Ahmad El-Rufai, wanda sanadiyyar haka ɗan tsohon gwamnan, Bashir El-Rufai, ya fito fili ya caccaki batun gwamnan cikin kakkausan lafazin, yayin da a ɓangare guda kuma yayansa, Bello El-Rufai, wanda ɗan majalisar tarayya na Kaduna ne, ya fito ya barranta da sukar da ya yi masa.

Haka kuma dambarwar ta kuma ci Shugabar Mata Na Jam’iyyar APC Reshen Jihar Kaduna, Maryam Suleiman, da aka fi sani da Maryam Mai-Rusau, saboda tsananin ƙauna da biyayya da ta ke yi wa tsohon gwamna, Nasir El-Rufai.

Yanzu dai da alamar komai ya kwaɓe tsakanin gwaskayen biyu tun bayan fallasa irin basukan da gwamnatin da El-Rufai ta ciwo ta bar wa gwamnatin Uba ta cigaba da biya.

Wannan kalamai da Gwamna Uba Sani ya yi ya jawo cece-kuce tsakanin magoya bayan ɓangarorin biyu. Wasu da yawa na ganin a matsayin Uba Sani wanda ya sha cewa ba shi da ubangida da ya wuce El-Rufai a baya, kuma da waɗanda suke ciki da wajen Jihar Kaduna sun san irin ƙoƙarin da El-Rufai ya yi ba dare ba rana domin tabbatar da Allah ya ba wa Uba Sani nasara a zaɓen 2023, bai dace ya fito fili ya riƙa goga wa tsohon gwamnan kashi a jika ba.

Kowa dai ya san irin yadda El-Rufai ya riƙa tsine wa Sanata Shehu Sani da Sanata Suleiman Hunkuyi, saboda sun ƙi saka hannu ya karɓi bashi daga waje.

Daga baya dai da koarfin tsiya da kuma qarfin gwamnati aka musanya Shehu Sani da Uba Sani, don a ciwo wannan bashi da yanzu ya ke kuka a kai.

Mohammed Bello El-Rufai, ɗan majalisar wakilan Nijeriya mai wakiltar mazaɓar Kaduna ta Arewa a majalisar wakilai ta 10, kuma ɗan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, ya samu rashin jituwa da ɗan uwansa, Bashir El-Rufai kan batun sukar da ya yi wa Gwamna Uba Sani.

Bashir a wani saƙo da ya wallafa a ranar Asabar ɗin da ta gabata, ya zargi Sani da yin watsi da alhakin da ya rataya a wuyansa ta hanyar ƙaurace wa jihar a kodayaushe da kuma zama a babban birnin tarayya Abuja.

Ya yi wannan zargin ne sa’o’i bayan da gwamnan jihar ya zargi tsohon gwamnan jihar, Nasir El-Rufai da barin tulin bashi na $587m da bashin N85bn da kuma kwantan kwangiloli 115 ga jihar, wanda hakan ya sa suke shan wahala wajen biyan albashi a cewarsu.

Yayin da Sani ya ce a shirye yake ya mayar da martani ga wannan suka da Bashir ke yi, sai babban yayansa, Bello, ya nesanta kansa daga sukar tare da jaddada biyayyarsa ga gwamna.

“Abu ne sananne a siyasa cewa wasu ba za su huta ba sai an yi faɗa tsakanin juna. Ina tsakiya, har ma zan iya ganawa da gwamna a daren yau cikin mintuna talatin.

“Makonni biyu da suka gabata, dole ne in kira ɗan uwana na gaya masa ya janye saƙon da ya wallafa a Tiwita. Na yi haka yau, amma ya qi. Ya haura shekaru 30. Jama’a su daina rikitar da hannayenmu.

“Ni mai biyayya ga Gwamna Uba Sani ne, kuma ba zan soke shi a fili ba. Ba wanda zai sa na yi haka. Ya ba ni hadimi, ya ba ni aikin gwamnati na farko, kuma ya yarda da zavena. Wannan kuma zai wuce. Ci gaban karkara da ake yi a Jihar Kaduna yana da ban sha’awa.

“Nijeriya gaba ɗaya, ba ma Kaduna kaɗai ba, na fuskantar matsalar kuɗi. A matsayinmu na shugabanni, an zave mu duka don yin abin da za mu iya da abin da muke da shi da kuma inganta shi. A gaskiya ban ga me hayaniya take ba.

“Gwamna shi ne shugaban jihar, kuma domin a bayyana gaskiya, duk da cewa Malam kamar yadda gwamna mai barin gado ya bayyana a cikin jawabinsa mai barin gado, nawa ne kuɗin da zai bari a jihar, na gwamna ne — bari na ɗauki hakan baya-haƙiƙa ne, ba shakka, don tabbatar da gaskiya, sanar da ‘yan ƙasa na jihar sanin yanayin kuɗi.

“Yanzu kuma, bari in fayyace, hare-haren da ake kaiwa a kafafen sada zumunta ba zai taɓa girgiza maigidana, Gwamna Uba Sani ba. Don haka, ‘yan hare-haren da mutane ke kaiwa kan wasu dalilai na zahiri da suka zo masa ba shi ne dalilin da ya yi abin da ya aikata ba.

Duk saboda wannan dambarwa, ita ma Shugabar Mata ta Jam’iyyar APC a Kaduna, Maryam Mairusau ta ƙalubalanci Uba Sani kan maganar da ya yi, inda hakan ta sa Jam’iyyar APC a jihar ta dakatar da ita saboda ta goyi bayan tsohon gwamnan jihar Nasir El-Rufai.

Maryam Suleiman, da aka fi sani da MaiRusau ta maida wa gwamnan da martani inda ta ce masa kuka bayan hari yake yi.

“Kuka bayan hari kake yi gwamna, za ka ce ba ka san da bashin ba ne lokacin da kake neman gwamnan ido rufe. Ka hana kowa zama kai ne can kai ne nan sai ka zama gwamna.

”Yanzu ka zama kuma yana neman ɗora wa tsohon gwamna laifi. Ai da baka nemi kujerar gwamnan ba.

”Tunda ka ce ba kuɗin da za ka yi aiki sai ka tarkata ka ƙara gaba, ka yi murabus kawai. Kuma ai da kai aka ciyo bashin kana kan gaba wajen ciyo bashin kuma yanzu ka zo ka ce wai ai babu kuɗi.”

Bisa waɗannan kalamai ne Jam’iyyar ta dakatar da ita ta ce za ta gudanar da bincike a kai.

Jam’iyyar ta ce akwai hanyoyi da dama da ya kamata Maryam ta bi a jam’iyyance domin warware irin matsala kamar yadda dokar jam’iyyar ta gindaya, ba kawai a hau shafukan sada zumunta ba ta riƙa surutai.

By Editor