Gargaɗin NDLEA kan ta’ammali da miyagun ƙwayoyi

A baya-bayan nan Shugaban Hukumar Yaƙi da Sha da Fataucin Muggan Ƙwayoyi ta Ƙasa (NDLEA), Mohamed Buba Marwa, ya ce, a cikin watanni 22 hukumar ta kama fiye da ƙwayoyin tramadol miliyan 100 na haramtacciyar hanya da sauran muggan ƙwayoyi masu cutarwa. Yawan shan waɗannan ƙwayoyi na varna da rayuwar al’umma musamman matasa, wanda ake saran al’umma za su fahimci ɓarnar da matsalar ke haifarwa.

Shugaban NDLEA, wanda ya bayyana hakan a yayin bikin bayar da lambar yabo da kuma ƙawata sabbin jami’an da aka ƙara wa girma a Abuja, ya ce, “A cikin qanqanin lokaci, hukumar ta kama masu safarar miyagun ƙwayoyi 23,907.”

A cewar hukumar, “kamun da muka yi ya haura tan 5,500 ko kuma kilogiram miliyan 5.5 na haramtattun ƙwayoyi, waɗanda aka kama tare da kuɗaɗen da sun haura Naira biliyan 450.”

Wani abin sha’awa, hukumar ta kai yaƙi da miyagun ƙwayoyi zuwa ƙofar masu noman tavar wiwi ta hanyar lalata gonakin tavar mai fazin hekta 772.5. A cikin watanni 22, ta hukunta sama da mutum 3,434.

Ɗaya daga cikin illar shan muggan ƙwayoyi shine haifar da matsalar tsaro. A halin yanzu an ɗora Nijeriya a matsayin ƙasar da ta fi hatsari a kan ayyukan ’yan ta’adda.

Abin takaicin shi ne yadda harkokin ’yan ta’adda ke ƙara ƙaruwa a kullum suna cin karen su babu babbaka, duk da cewa, babu wani sashe na duniya da ya tsira daga abubuwan da suka shafi ayyukan ’yan ta’adda amma lamarin Nijeriya yana da ban tsoro.

Don nuna jajircewarsa a kan yaƙi da miyagun ƙwayoyi, tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya ƙaddamar da shiri na musamman da aka yi wa laƙabi da ‘War Against Drug Abuse” (WADA)’ da kuma kundi na musanmman mai suna “National Drug Control Master Plan 2021-2025” na yadda za a fuskanci yaƙi da miyagun ƙwayoyi a sasan ƙasar nan.

Buhari ya kuma ce, barazanar da miyagun kwayoyi ke yi wa qasar nan ya fi na ayyukan ta’addanci da ake fuskanta.

Mun amince da bayanin shugaban ƙasa na cewa, miyagun ƙwayoyi ya taimaka wajen ƙara zafafa ayyukan masu garkuwa da mutane da ’yan ta’adda a sassan Nijeriya, mun kuma amince da irin nasarorin da NDLEA ke samu a yaƙi da miyagun ƙwayoyi, muna kuma kira da a ƙara ƙaimi wajen zafafa yaqin da ake yi da masu safara da mu’amala da miyagun ƙwayoyi a sassan ƙasar nan ta haka za a tabbatar da rage lamarin yadda ya kamata.

Wannan yaƙi na kowa da kowa ne, saboda haka muna kira ga iyaye, makarantu da ƙungiyoyi masu zaman kansu da sauran al’umma gaba ɗaya da su kawo nasu gudunmawar don samun nasarar fatattakar masu safarar ƙwayoyi da masu ta’ammali da ita, tare da kuma ba hukumar NDLEA goyon bayan da take buƙata gabaɗaya.

Babu shakka, shawarar da mahukuntan hukumar suka yanke na yin amfani da na’urorin wajen inganta martabar hukumar na iya haifar da gagarumar nasara ga hukumar. Don haka ne hukumar NDLEA ƙarƙashin jagorancin Marwa ta ƙuduri aniyar yin duk mai yiwuwa don inganta ayyukan da ake yi. A bara, NDLEA ta ƙara wa jami’ai 3,506 ƙarin girma. A bana, an ƙara wa jimillar jami’ai 1,018 ƙarin girma zuwa sabbin muƙamai.

Marwa ya yi amfani da wannan dama wajen yabon shugaban ƙasa Bola Tinubu, wanda irin goyon bayan da yake bai wa hukumar ta sa aka samu nasara a aikin da ya ba ta. A yayin da muke yaba wa Tinibu kan ƙudirin kawar da miyagun ƙwayoyi a ƙasar nan, muna roƙonsa da ya fitar da miliyoyin ’yan Nijeriya daga ƙangin talauci ta hanyar samar da ayyukan yi masu yawa da sauran matakan rage raɗaɗin talauci.

Mun faɗi haka ne saboda akwai wata alaƙar da ba za a iya raba ta ba tsakanin ƙaruwar talauci a ƙasar da ƙaruwar amfani da muggan ƙwayoyi. Muna kira ga al’umma da su guji ta’ammali da muggan ƙwayoyi domin gujewa faɗawa aikata laifuka.