‘Ba ka da ƙwarewa, sai tarin hadimai mara kan-gado’ — martanin ɗan gidan El-Rufa’i ga Gwamnan Kaduna

Daga BASHIR ISAH

A wani yanayi mai kama da martani, ɗan gidan tsohon Gwamnan Jihar Kaduna, Bashir El-Rufai, ya zargi Gwamnan Kaduna, Uba Sani, da rashin zama a jiharsa don yi talakawansa aiki sannan ya koma ya tare a Abuja.

Haka nan, ya zargi Gwamna Sani wanda aboki ne ga mahaifinsa, da cewa ya tara hadimai mara kan-gado waɗanda ba su da ƙwarewa balle kuma su suka shi a hanya.

Ya ci gaba da cewa, maimakon Gwamnan Kaduna ya yarda da rashin ƙwarewarsa, amma ya ɓuge da yin ƙorafi kan cewa ya gaji tulin bashi daga gwamnatin El-Rufai.

Tun da fari MANHAJA ta rawaito labari a kan yadda Gwamna Sani ya bayyana tarin basussukan da ya ce ya gada daga gwamnatin da ya gada.

Basussukan da ya ce sun haɗa da $587m da N85bn da kuma kwangiloli 115.

Ya bayyana hakan ne a wajen taron jin ra’ayoyin mutanen gari kan shugabancinsa wanda aka shirya a ranar Asabar da ta gabata.

Biyo bayan wannan furuci da Gwamnan ne aka ji ɗan gidan El-Rufai, wato Bashir El-Rufai ya mayar da martani kan kalaman Gwamnan a shafinsa na X, inda ya bayyana Gwamna Sani da tawagarsa a matsayin waɗanda ke fama da rashin ƙwarewa.

Bashir ya bayyana mamakinsa kan yadda Gwamna ya ɓuge da ba da uzirin cewa nauyin bashin da ke kan gwamnati ya hana su taɓukawa yadda ya kamata.

“Waɗannan mutanen sun fahimci cewa ba su da ƙwarewa gaba ɗaya, kuma hanyar da za su rufe maganar ita ce karkatar da tunanin jama’a.

“Daga kan Gwamnan da kullum yana Abuja zuwa tarin masu taimaka masa waɗanda ba su iya aiki ba, waɗanda aka bai wa muƙamai saboda dalilai na siyasa,” in ji Bashir