Na gaji tarin basussuka daga gwamnatin El-Rufai, cewar Gwamnan Kaduna

Daga BASHIR ISAH

Gwamna Uba Sani na Jihar Kaduna ya bayyana cewa, ya gaji ɗimbin basussuka daga gwamnatin da ya gada, lamarin da ya ce taliƙe kaso mai tsoka daga kason wata-wata da jihar ke samu a wajen Gwamnatin Tarayya.

Basussukan da ya ce ya gada faga gwamnatin Nasir El-Rufai sun haɗa da Dala Miliyan 587 da Naira Biliyan 85 sai kuma kwangiloli guda 115.

Gwamna Sani ya bayyana haka ne a wajen taron jin ra’ayoyin jama’ar gari dangane da shugabancinsa da aka shirya ranar Asabar.

Ya ce, ba zai yi ƙasa a gwiwa ba wajen yin amfani da ɗan abin da kan rage wa jihar wajen aiwatar da ayyukan cigabanta.

Da yake jawabi a wajen taron, Kwamishinan Kuɗi na Jihar, Shizzer Bada, ya yi wa taron jawabi a kan abin da jihar ke samu daga asusun tarayya da kuma kason da ake ɗebewa don biyan basussukan da gwamnatin da ta gabata ta kinkimo.

Mahalarta taron sun haɗa sarakunan gargajiya da ‘yan siyasa da Ƙungiyar Ƙwadago (NLC) da ƙungiyar matasa da sauransu.