Tattalin arziki: Tinubu ya fara haifar da ɗa mai ido – Ministan Labarai

Daga MAHDI M. MUHAMMAD

Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Mohammed Idris ya ce sauye-sauyen tattalin arziki da gwamnatin shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke jagoranta sun fara samar da ɗa mai ido.

Ya bayar da misali da cigaba aka samu a cikin ‘yan kwanakin nan.

Ministan ya yi wannan jawabi ne a wajen babban taron ƙoli na masu magana da yawun hukumomi, wanda Cibiyar Hulɗa da Jama’a ta Nijeriya (NIPR) ta shirya a Abuja.

Ya ce, “Abin farin ciki ne a lura da cewa sauye-sauyen tattalin arziki da shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ke aiwatarwa na samun ƙarin nasarori a ɓangarori daban-daban na tattalin arzikinmu, wanda ke nuni da ƙudurinmu na magance matsaloli masu mihimmanci kamar hauhawar farashin kayayyaki, daidaiton kuɗaɗen waje, jawo hankalin ƙasashen waje kai tsaye a zuba jari, haɓaka asusun ajiyar mu na ƙetare, tallafin man fetur a tsakanin sauran shirin cigaban tattalin arziki. “

Idrsi ya ƙara da cewa, “Taron wani muhimmin taro ne da nufin kawo sauyi a fannin sadarwa a Nijeriya.”