Daga MAHDI M. MUHAMMAD
Tsohon Ministan Yaɗa Labarai da Wayar da Kai, Lai Mohammed, ya bayyana yadda labaran ƙarya a shafukan sada zumunta suka kusan raba shi da matarsa da suka shafe sama shekara 40 suna tare.
Tsohon ministan ya bayyana hakan ne a Legas a wani taron tunawa da cika shekaru 90 na wanda ya tava lashe kyautar rubuta a fannin adabi a Afirka, Farfesa Wole Soyinka.
Mista Mohammed, abokin tafiyar da kamfanin Bruit Costard, mai fafutuka kuma kamfanin hulɗa da jama’a, ya tuna cewa ɗaya daga cikin ƙalubalen da ya fuskanta a ofis a matsayinsa na minista shi ne labaran ƙarya, bayanan ƙarya da yaɗa labarai.
Da yake magana musamman kan yadda lamarin ya kusa lalata aurensa, Mista Mohammed ya jaddada cewa illar labaran ƙarya da ƙarya da kuma bayanan ƙarya na da matuƙar illa.
“Ku ba ni dama in bayyana muku a bainar jama’a a karon farko, yadda kafafen sada zumunta suka yi barazana ga rayuwar aurena na shekara arba’in. Wani lokaci a cikin 2018 ne na zo Legas daga Abuja don aikin hukuma. Kamar yadda na saba, na kwanta barci misalin tsakar dare, amma misalin qarfe 3:00 na safe, matata ta tashe ni daga barcin da nake yi. Da farko, na firgita, ina tsoron cewa an samu matsalar tsaro, amma tunanin matata ya musanta hakan, domin ta natsu tana magana,” inji tsohon ministan.
Mista Mohammed ya ce zargin da matarsa ta yi, wanda, a cewarsa, “bam ne” da aka ba shi labarin a cikin harshen Yarbanci, amma an fassara shi kamar haka:
“Baba, mutuwa za ta iya zuwa a kowane lokaci; don Allah ni ma a matsayina na matarka, in kasance mai sanya hannu kan asusun ajiyar ka na ƙetare na Ali Financial, wanda ya ƙunshi dala biliyan 1.3.’’
