A ceci al’ummar Borno kafin labarin mutuwa ta riske ku

Gari yayi zafi, ta ko ina ta ɗauki ɗumi. Rayuwa na sake yin tsada, komai na ta ƙaranci, hakan ya sa dole sai an shiga motar Zulum, wanda cunkusuwa ya yi yawa, hakan na iya sa mutane su rasa rayukan su.

Kwamishina mai kama da agogo, wanda yana tare da Gwamna mai alfarma kuma mai tausayin al’umma. Nace tausayi, wanda kowa yasan an gani, kuma lallai an shaida. Ba a kammala wanka sai da sabulu, dole a duba lamarin nan don gyara adon amarya a gaban angon ta.

Abubuwa da ke faruwa;

  1. Mutane na tururuwa cikin motar nan, ana matsi sossai, kujerar da ya kamata a dau mutum biyu ana ɗaukan 3. Babu iska mai kyau, ga mata, ga masu goyo, wallahi har da mace mai ciki na bin sahun shiga motar nan.
  2. Cin mutunci drebobi ga marasa galihu. Na taba shiga motar, naga wani dreba yana zagin mata kamar yara ƙanana, wallahi ciki har da wanda ta haife shi, na zubar da hawaye ranar.
  3. Na tava ganin wata mata, ta zo da goyo, ga kaya aka, ga kuma zafin rana, ta zo za ta shiga, masu lodi suka tunkuɗa ta zuwa waje da kayan ta, na tambaya cemin akai wai dreba ne. Yana ta rantsuwa ba zai ɗauke ta ta, wallahi na ji takaici sossai.
  4. Su kan su direbobin, suna cikin yanayi, fasinja zai iya sauka anana, wani kuma a gaba kaɗan. Suna wasu na kokawa game da tsarin na aikin na rashin mai ko haraji da aka ɗaura musu. Da wannan ne ma suke kafa hujjar yin lodi da tafi ƙarfin motar.
  5. Ɓarayi sun yi yawa, yanzu-yanzu su buga mota, ba don komai ba face don kawai su saci kayan fasinja.
  6. Wani kalar kuɗi da ake anfani da su, na kasa gane wai ina ne wannan kuɗin ya fito. Musamman wajen neman canji ana ta samun gagarumar matsala.

Hanyoyi da ta kamata abi wajen magance wannan!

A tunani na ya kamata ace;

  1. A dawo da anfani da Bus-Stop, mutum ba zai sauka ba sai a Bus-Stop, kuma ba zai hau ba sai a can.
  2. A kawo tsarin Legas, jiha ai jiha ce, babu batun cewa za mu samu cigaba da za a yi hakan ba. Mutum ya biya kuɗi a Bos-Stop kafin ya shiga mota. Za ka iya yin booking ma, hakan zai ba da dama ga masu tiransifa, saboda yanayi da ake ciki ma rashin isassun takardun kuɗaɗe a hannu. Mutum ya biya kuɗin, ya zo ya nuna takardar shaida, sannan ya a bar shi ya shiga mota. Hakan zai taimakawa fasinja da kuma drebobin motar.
  3. A qayyade yawan mutane da motar zata ɗiba. Misali idan mutum 30 ne, to ba su lodi za su dubi iya mutum 30 sannan su tafi, wani motar kuma tazo da ɗibe su. Hakan zai sa, a magance yamutsuwa da ake yi a cikin motar. Mai ciki za ta samu sa’ada, raunana kuma a ba su haƙƙin su.
  4. Drebobin su kula da haƙƙin mutane, banda cin mutunci, ban da raina iyaye, musamman ma mata da suka haife su. Ga fasinja, bai kamata ya zo yana cacar baki da direba ba.
  5. Idan babu, ko ana ƙarancin takardun kuɗaɗe, tsarin yin tiransifa zai matuƙar taimakawa al’umma.
  6. Ban ce ba, amma ya kamata, ban kuma ce dole ba, ko ba a yi tsarin ba yana da kyau. Wannan tsarin shi ne, tsarin dawo anfani da kati, mutum yana zuwa kawai na’ura za ta tantance shi sannan ya kwaɗe mota abun shi. Idan ya zo sauka motar ta ce masa Goodbye legend, ko a sauka lafiya da Hausa, yayin da daman lokacin zai shiga an ce masa welcome.

Wannan shi ne taƙaice mai girma kwamishina.

Akwai tsare-tsare masu yawa, wanda Yakamata a ɗauki mataki akai, kafin aji cewa za fi ya sa wata mata ta mutu a motar Zulum. Ko ace wata ta haihu saboda cunkoso, ko ace jaririn yaro ya mutu saboda turmutsutsu.

Allah ya sa mu dace, Allah ya ƙara lafiya. Shawara ce, ba umarni ba.

Wasiƙa daga MUHAMMAD ALBARNO.08034400338.