Ina yayu da ƙannen Emefiele?

Daga NASIRU ADAMU EL-HIKAYA

A gaskiya sunan tsohon gwamnan babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele ke kan gaba a zahiri a yanzu cikin jami’an tsohuwar gwamnatin Buhari da a ke tuhuma da rub da ciki da dukiyar al’umma. Ba a yi mamakin hakan ba don zarge-zarge da a ke yi ma sa na murɗiya tun ma gabanin shigowar tsohon shugaba Buhari mulki a 2015.

A iya tunani da duba tarihi Emefiele zai zama cikin na kan gaba da su ka fi daɗewa kan wannan kujera ta gwamnan babban banki. Ya yi aiki da shugabanni 3 na dimokuraɗiyya kuma an haƙiƙance ya so shi kan sa ya zama shugaban ƙasa alhali bai yi murabus daga babbar kujerar da ya ke kai ba. Ya ɗauki mafi tsaurin mataki a tarihi na canja kuɗi da ya yi matuƙar kuntatawa al’ummar ƙasa ba talakawa ba masu hannu da shuni. Sai bayan saukar shugaba Buhari ne ma ya ke ƙarin haske da cewa don hana amfani da kuɗi a wajen zaɓe ne ya sa xaukar matakin.

Shin matakin ya taimaka wajen hana maguɗin ko bai taimaka ba ita dai jam’iyyar APC ta Buharin ce ta zarce a karagar mulki.

A kaikaice a iya cewa gwamnatin Buhari na ɗaukar APC a matsayin jam’iyya mai gaskiya da riƙon amana duk da dai yau shi kan sa wanda ya aiwatar da canjin kuɗin na cikin zargi dumu-dumu na wawure kuɗi har ma da mallakar bankuna. Haƙiƙa in akwai wanda wannan shirin ya taimaka to jam’iyyar APC ce. Hatta shugaba Tinubu da a ke cewa an ƙirƙiro shirin ne don yi ma sa zagon ƙasa a samun madafun iko to ai ya samu sai me kuma? wasu ɗaiɗaikun ‘yan majalisa ko wasu tsoffin gwamnoni ba su lashe zaɓe ba ba wani babban abun misali ba ne don majalisar dattawa na cike da tsoffin gwamnonin da wasun su na rayuwar gidan gilashi don gudun bita-da-ƙulli.

Shi ma kan sa shugaban majalisar na yanzu Godswill Akpabio tsohon gwamna ne kuma lokacin da ya zama ministan Neja Delta majalisa ta yi ta neman sa amma tamkar ya yi biris da ita. Wane canji a ka samu da canjin kudi fiye da azabar da talakawa su ka sha har da rahoton asarar rai.

Wannan ma fa ba ra’ayin tsohuwar gwamnatin ba ne dakatar da shirin mai tsauri sai da wasu gwamnoni su ka kai ƙara kotu. An soke shirin ko ba a soke shi ba ya dai shiririce wanda ya sha azaba kuwa ba mamaki sakamako sai dai gobe kiyama gaban Sarkin da ba shi da Waziri.

Abun ka da shirin gwamnati in ta dauko abu ko ba shi da ma’ana sai ta aiwatar kuma a samu wasu ‘yan ma’abba su shafawa fuskar su toka su na ƙarewa. Da wuya ka ga sabon kuɗin da a ke magana an canja ko an yi wa fenti tsoffin takardun ne a ke amfani da su.

Ni na ga wasu daga kudin da a ke cewa sabbi ne sun tsufa. A gani na akwai buƙatar fitowa fili a ba wa al’ummar Nijeriya haƙuri kan ragaitar da su ka yi kan wannan shiri da a ka so da farko a ce muradin sa shi ne hana ɓarayin daji amfana daga kuɗin da ke hannun su tun da ba mamaki ba za su iya shigowa gari don yin canji ba.

Wani abun ma shi ne a lokacin mutane sun yi ta ƙoƙarin ɓatar da tsoffin kuɗin ta hanyar sayan abubuwan da ba sa buƙata hakanan don neman takardun kuɗi wasu sun karyar da kayan su masu tsada kan kuɗi ƙalilan. Tuna wancan lokacin ma kan iya saka mutum tashin balli-balli don wuyar ba ta misaltuwa.

Abun da mutane za su so gani shi ne ina sauran muqarraban Emefiele a yayin da ya yi wancan dogon aiki ko dai ƙarancin waɗanda a ke zargi na da hannu wajen zambar ce ya sa a ke jin sunaye ƙalilan nan ma ba wani shaharerre daga tsoffin masu riƙe da madafun iko?

A can baya dai akwai wasu mutum biyu da rahoton bincike ya nuna Emefiele ya yi amfani da su a matsayin ‘yan baranda wajen mallakar wasu bankuna. Mutanen da a ka ba da labari dai Mr.Rahul Savara da Cornelious Vink ba a sake jin duriyar su ba.

Bayanin ya nuna su su ka samar da kuɗi wajen kafa bankin Titan Trust da ta bayan fage rahoto ya tabbatar mallakar Godwin Emefiele ne. Zuwa yau ba mu ji wani jami’in tsohuwar gwamnatin ya wanke ko ya nesanta gwamnatin daga zarge-zargen da a ke yi wa Emefiele ba. Gaskiya da son samu ne matuƙar dai yaƙi da cin hanci da rashawa ya yi nasara a ƙarƙashin gwamnatin da ta shuɗe da a na gaiyatar Emefiele ne a na ba shi lambobin girma don namijin ƙoƙarin da ya yi wajen riƙe amanar al’umma.

Tun a juyin mulkin soja da ya kawar da marigayi Shehu Shagari a ke jin tsohon shugaba Buhari na kokawa kan cin hanci. Akwai ma shaharerren kaulin sa da ke cewa “in ba mu kashe cin hanci ba cin hanci zai kashe Nijeriya” kazalika tsohon shugaban ya ce “ba mu da wata kasa face Nijeriya don haka sai mu cece ta tare” wato ma’ana daga almundahana da sauran abubuwan da kenan su ka kawo tarnaqi wajen cigaban ƙasar.

Ni kuma wallahi da za a ba ni zaɓi da sai na ce in zai yiwu a maida Nijeriya yanda sojoji su ka same ta a jamhuriya ta biyu daga 1979-1983 da ya fi alheri don ni ban ga wata nasara da a ka cimma da ta share alheran jamhuriya ta biyu ba da wasu su ka zayyana da ta ‘yan cin hanci da rashawa. Kowa ya yi bitar lokacin musamman ma waɗanda a ka dama da su da ƙuruciyar su a lokacin za su gano farashin dala da na kayan masarufi da ma masana’antu a Nijeriya. Kai hatta darajar Nijeriya ma ƙetare a lokacin ba ta samu koma baya ba irin yanzu.

In akwai cigaban da a ka samu bai fi na sabbin ‘yan jari hujja da a ka yi mu su rejista ba. In wani ya kawo batun wayar salula ko na’ura mai kwakwalwa da yanar gizo, sai in ce duk waɗannan ba a Nijeriya a ka ƙirƙiro su ba. Farkon shekarun 1980 abinci ba ya gagarar talaka sai dai wataƙila wani na ci da nama wani kuma lami. Yau nama ko na ce lamin miliyoyi ke buƙata amma ba sa samu. Tsaro kuma a lokacin in an kwatanta da zamanin da mu ke ciki za a iya cewa rayuwa a waɗancan shekarun tamkar aljannar duniya ce. Ka ratsa dazuka dare da rana ba irin wannan mummunar fargaba.

Gwamnatin Nijeriya ta Bola Tinubu na duba rahoton babban mai binciken ayyukan bankin ƙarƙashin tsohon shugaba Buhari.

Wannan na zuwa ne bayan kammala aikin mai binciken na musamman Jim Obazee da miƙa rahoto fadar Aso Rock.

Tun gabanin kammala rahoton an saki wasu bayanai na abubuwan da Obazee ya gano ciki da bankaɗo cewa tsohon gwamnan bankin Godwin Emefiele na mallakar wasu bankuna da kuɗin almundahana baya ga kafa bankin TITAN TRUST.

Abun da a ka aara fahimta daga rahoton shi ne zargin Emefiele da azurta wasu ‘yan lele da ba su canjin dala a farashin gwamnati don cin ƙazamar riba.

Mai taimakawa shugaba Tinubu kan labaru Abdul’aziz Abdul’aziz ya ce gwamnatin ba za ta lamunci aiyukan badaƙala ba “to kamar yadda ka sani shi wannan kwamiti ya na da aiki wanda ya ke mai matuqar faɗi mai yawa kuma sun miƙa kammalellen rahoto a kan badaƙalar da a ka yi a babban bankin Nijeriya a waɗancan tsawon shekaru.

Gwamnati za ta duba domin ɗaukar mataki na gaggawa domin a tabbatar da cewa dukkanin waɗanda su ka yi ba daidai ba an hukunta su kuma an kwato dukiyar jama’a da ta shiga hannun da bai kamata ba.”

Lauya mai zaman kan sa a Abuja Mai Nasara Kogo Umar na daga waɗanda su ka bi diddigin aikin Obazee da ba da shawarar gwamnati ta aiwatar sakamakon rahoton “hurumi na sashe na 15 sakin layi na biyar na tsarin mulkin Nijeriya wanda ya dace dole ne kowane jami’in hukuma ya yaƙi cin hanci da rashawa da kuma amfani da kujera don gina kai. Shi Emefiele nan wurin ya yi amfani da kujerar shi ne domin ya gina kan shi.”

Emefiele a na sa ɓangaren na musanta aikata laifi duk da ba za a iya sanin abun da ke gudana kan tuhumar a bayan fage ba.

In za a tuna mai ba wa shugaba Tinubu shawara kan siyasa Ibrahim Masari ya ce sam ba za a saurarawa Emefiele kan tuhumar gagarumar badaƙala ba “tsohon shugaban babban bankin Nijeriya Godwin Emefiele yadda ya cutar da bayin Allah, ya karya bayin Allah ya yi abun da ya yi; ashe wannan mutum azzalumi ne ya wawure kuɗaɗen talakawan Nijeriya.”

Emefiele na fuskantar tuhumar a gaban babbar kotun birnin taraiya Abuja da ta Lagos.

Yanzu haka ya na hannun hukumar yaqi da cin hanci EFCC a Lagos har ya kai inda kotu za ta duba buƙatar ba da belin sa kan tuhumar karkatar da biliyoyin dala.

Kammalawa;

Inda duk hukumomin bincike za su yi adalci ko a bar su su yi adalci kan rahoton Jim Obazee to da ba mamaki a samu wani sauyi mai ma’ana. Kazalika in shari’a ko alƙalai za su yi hukuncin ba sani ba sabo to nan ma ƙarin nasara ne. Babban abu shi ne adalci ga kowane ɓangare da zai zama silar gyara qasa. In ma a baya an samu kuskure ko sakaci wajen adalci to ban ga wani uzuri a yanzu na gaza tauna tsakuwa don aya ta ji tsoro ba.