An kama mutum 20 bisa mamaye sakateriyar gwamnatin Oyo

Daga NASIR S. GWANGWAZO a Abuja

Yan sanda tare da haɗin gwiwar wasu Jami’an tsaron sun cafke mutum ashirin da ake zargin sun mamaye/kai hari harabar gwamnatin a Agodi, Ibadan ranar Asabar.

An sami amsar harsashai, da katin ATMs daga waɗanda ake zargin.

“Baki daya, mutum ashirin aka kama wanda ake same su da bindiga 3, da harsashi 291, adduna 67, rigar kariya daga harsashi guda 5, takalma 6, amsa kuwa guda 10, hula nau’in odua nation guda uku, maɗaurin ƙugu guda 7, kayan soja nau’in Odua nation, mota ƙirar nissan marar rajista, sai talabijin 3 da mashina guda 3” a cewar mai magana da yawun yan sanda shiyar oyo da ya fitar a wata sanarwa.

Rundanar yan sanda tace, masu mamayar a na zargin su da zama yan ƙungiyar Jamhuriyar Yarabawa wanda tace yin hakan a mastayin babban laifi kuma rashin kishin ƙasa ne. Laifi ne wanda ya nuna tsantsar cin amanar ƙasa da kuma ta’addanci wanda za ai hukunci dai dai da dokokin ƙasa.

A cewar yan sandan, an ƙaddamar da bincike a kan lamarin. Masu binciken sun haɗa da, mataimakin kwamishinan yan sanda mai kula da sashin manya laifukan na jihar.

Maharan sun iso wajen ne a motoci ƙirar bus wanda sukai yunƙurin ƙutsa kai cikin ofishin gwamna a yayin harin amma bisa jajircewar jami’an tsaro ba suyi nasara ba.

Sun sanya abun rufe fuska, sannan suka ɗaga tutar kungiyar ƙasar yarabawa a yankin yayin harin da ya afku da sanyin safiya.

Waɗanda ake zargi, waɗanda ke sanye da kayan sojojin sun zo ne da manyan makamai a wata mota marar rajista ƙirar nissan wanda a cikinta akwai adduna, bindigogi, wasu siddabaru da kuma tutar ƙasar Oodua ” a cewar yan sandan.

A yayin harin, haɗakar jami’an tsaro da sojoji sun bazama a wannan yankin inda suka rufe hanyar shiga da fita na sakateriyar gwamnatin. Daga nan sai aka juya akalar masu ababen hawa daga wajen.

Shaidu sun ce sun ji harbin bindiga wanda ya faru sanadiyar musayar wuta da jami’an tsaro da maharan.

Komai ya dawo dai dai a sakateriyar domin har an hangi wasu na shagulgulan su a harabar gidan jagoran.