Za mu ƙarfafa wa sojoji kan yaƙi da ta’addanci a Zamfara — Tinubu

Daga BASHIR ISAH

Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya jaddada ƙudirin gwamnatinsa kan yaƙi da ta’addanci a Jihar Zamfara.

Tinubu ya ba da odar tura ƙarin sojoji zuwa jihar a matsayin mataki na ƙarfafa wa sojoji gwiwa wajen yaƙi da ɓarayin daji a jihar.

Bayanin haka na ƙunshe ne cikin sanarwar manema labarai wadda mai magana da yawun Gwamnan Zamfara, Sulaiman Bala Idris, ya fitar a ranar Asabar.

Sanarwar ta ƙara da cewa, Tinubu ya ƙarɓi baƙuncin wasu gwamnonin jihohi da kuma shugabancin Majalisar Tarayya a gidansa da ke Legas.

Ta ce, gwamnonin sun kai ziyarar ne a ranar Juma’a ƙarƙashin jagorancin Mataimakin Shugaban Ƙasa Kashim Shettima, da zummar miƙa gaisuwar sallah ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu.

“A tattaunawarsu da Gwamna Dauda Lawal yayin ziyarar, Shugaba Tinubu ya yi tuntuɓa dangane da halin tsaron Jihar Zamfara ke ciki.

“Gwamna Lawal sanar da Tinubu cigaban da aka samu da kuma ƙoƙarin da sojoji ke yi wajen fatattakar ɓaraysin daji a jihar.

“Daga nan Shugaba Tinubu ya bai wa gwamnan tabbacin himmarsa wajen kawo ƙarshen ‘yan fashin daji a jihar, ya ƙara da cewa ya ba da umarnin tura ƙarin sojoji zuwa jihar.

“Tinubu ya buƙaci Gwamna Lawal ya riƙa ba shi bayani lokaci-lokaci dangane da halin tsaron jihar da nufin samun haɗin kai da daidaito game da yaƙi da ɓarayin daji,’ in ji sanarwar.