‘….Mu taimaka wa Adam Zango da soyayya a halin da yake ciki’

Daga FAUZIYYA D. SULAMAIN

Ban taɓa magana a kan wani ɗan fim ba, amma halin da Adam Zango ke ciki yana buƙatar mu nuna masa soyayya irin ta addini. Yana buƙatar mu ja shi a jiki, abubuwan da ya ke yi a yanzu akwai damuwa.

Don Allah a samu waɗanda za su je kusa da shi don Allah, komai zai iya faruwa da shi, domin a yanzu yana ruguza gidansa da rayuwar yaransa da danginsa da ‘yan’uwansa.

Amma don Allah mu ja shi a jiki, kar mu ji haushinsa yana buƙatar kulawar duk wani musulmi hakan zai dawo da shi daidai ya fita daga damuwar da ya ke ciki.

Mu yi haƙuri mu kawar da kai ga komai, don Allah a samu masu zuwa kusa da shi please kafin abunnan ya gama lalacewa.