Sau uku ina kama matata da aikata baɗala — Zango

Daga BASHIR ISAH

Jarumi a masana’antar Kannywood, Adam A. Zango, ya bayyana cewa sau uku yana kama matarsa da aikata baɗala, amma duk da haka ya yi haƙuri ya ci gaba da zama da ita.

An ji jarumin ya bayyana haka ne a cikin wani faifan bidiyo.mai tsawo da aka yaɗa a soshiyal midiya.

A cikin bidiyon, jarumin ya taɓo batutuwa da dama, daga ciki har da yadda wasu abokan sana’arsa waɗanda ya taɓa bai wa gudunmawa a rayuwa ba sa ba shi kariya ga mutuncinsa da kuma irin rashin haɗin kan da ke Kannywood.

Haka nan, Jarumin ya taɓo abin da ya shafi cikin gidansa, inda ya ce, “na kama matata da laifin yin ɗan malele amma na ci gaba da zaman aure da ita.

“An tura min bidiyon batsa da matata ta yi da kanta, a kan na biya naira milyan ɗaya ko a saka a duniya na yi haƙuri na ci gaba da zaman aure da ita.

“Na kama matata da cin amanata da ɗan uwana, na yi haƙuri na ci gaba da zaman aure da ita.

“Idan na yi musu ƙazafi Allah Ya tona min asiri tun a duniya.

“Ku gaya min maza nawa ne masu imanin da za su iya haƙuri kamar yadda na yi,” in Zango.

Wannam ala’amari ya ɗauki hankalin masoyan Jarumin da ma abokan sana’arsa, inda tuni wasunsu suka fito suka bai wa jarumin shawarwari tare da tausasa shi kan ya ƙara haƙuri dangane da halin da ya tsinci kansa