Mutum 3 sun mutu, 12 sun jikkata sakamakon rikici tsakanin sojoji da matasa a Yobe

Daga MUHAMMAD AL-AMEEN a Damaturu

Biyo bayan wata hatsaniyar da ta ɓarke tsakanin sojoji da ‘Yan Adai-daita Sahu (Napep) a garin Gashuwa, shalkwatar ƙaramar hukumar Bade dake jihar Yobe, ya jawo asarar rayukan mutum uku tare da raunata mutum 12 a ranar Lahadi.

Bayanan da wakilinmu ya tattaro sun nuna cewa, hatsaniyar ta ɓarke ne sakamakon wata rashin jituwar da ta ɓarke tsakanin sojojin da Yan Adai-daita Sahun bayan nuna rashin jin daɗi kan matakin da sojojin suka ɗauka na halaka wani matuƙin Keke Napep.

Wata majiya a Babbar Asibitin Ƙwararru da ke garin Gashuwa ta bayyana cewa, an kawo gawar mutum uku, tare da ƙarin mutum 12 waɗanda suka samu raunuka daban-daban, a hatsaniyar.

Wani mazaunin garin da abin ya faru a gaban idonsa wanda ya buƙaci a sakaya sunansa, ya bayyana cewa, “Abin da ya faru shi ne motar sojojin ce ta zo a guje, inda ta yi kiciɓis da motar Golf, a ƙoƙarin kaucewa ne soja ɗaya ya faɗo, inda motar sojojin ta kaɗe wani Keke Napep, wanda hakan ya jawo sojojin ɗaukar mummunan matakin.”

“Wannan ya jawo matasan su ka harzuƙa tare da kulle babbar hanyar, ba shiga ba fita. Hakan ya jawo Shugaban Ƙaramar Hukumar Bade, Hon. Ibrahim Babagan Yurema, haɗi da Maji-daɗin Bade zuwa wajen domin bai wa matasan haƙuri don hana tashin-tashina.”