Walin Zazzau kuma Hakimin Ikara, Aminu Umar ya kwanta dama

Daga BASHIR ISAH

Majalisar Masarautar Zazzau ta sanar da rasuwar Walin Zazzau kuma Dagacin Ikara, Engineer Aminu Umar.

Sanarwar ta ce marigayin ya rasu ne bayan kammala bukukuwan sallar da masarautar ta shirya albarkacin Ƙaramar Sallah.

Marigayi Umar ya fito ne daga zuriyar marigayi Sarki Dalhat daga daular Barebari ta Masarautar Zazzau.

A halin rayuwarsa, ya taɓa riƙe muƙamin Shugaban Hukumar Ruwar ta Jihar Kaduna.

Da yake tabbatar da rasuwar marigayin, mai magana da yawun masarautar, Abdullahi Aliyu Kwarbai, Marigayin ya halarci Hawan Daushen da Masarautar Zazzau ta shirya a ranar Juma’a.

Kuma yana ɗaya daga cikin sarakan da suka kai wa Sarkin Zazzau, Malam Ahmed Nuhu Bamalli, gaisuwar Sallah.

Marigayin ya rasu ya bar mata da ‘ya’ya. Kuma an yi jana’izarsa daidai da karantawar Musulunci a ranar Lahadi.