Gwamna Lawal ya zama ‘Wakilin Ƙauran Namoda’

Daga BASHIR ISAH

An naɗa Gwamnan Jihar Zamfara, Dauda Lawal, sarautar Wakilin Ƙauran Namoda.

Wannan na zuwa ne biyo bayan Hawan Daushen da Gwamna Lawal ya halarta a ranar Lahadi wanda Ƙaramar Hukumar Ƙauran Namoda a jihar ta saba shiryawa duk shekara lokacin bikin sallah.

Kakakin Gwamna, Sulaiman Bala Idris, ya ce hawan daushe a lokacin bikin sallah kan haɗo kan jama’a wuri guda don gudanar da bukukuwa da raya gargajiya.

Sanarwar manema labarai da Sulaiman ya fitar ta ce, an naɗa Gwamna Lawal a matsayin ‘Wakilin Ƙaura’, wanda ke nufin mai wakilcin wanda ya kafa masarautar.

A cewar sanarwar, “A yau Gwamna Dauda Lawal ya halarci hawan daushe wanda Masarautar Ƙauran Namoda ta saba shiryawa shekara-shekara.

“Hawan Durbar biki ne mai cike da ƙawa wanda ke nuni da kyawawan al’adun Masarautar Ƙauran Namoda. Hawan Durbar a yankin Ƙaramar Hukumar Kauran Namoda na bai wa jama’a damar haɗuwa wuri guda don sada zumunta da farin ciki da kuma bikin shekara.

“An ga Gwamna Lawal a wajen bikin sanye da kayan sarauta na gargajiya kuma a kan dokin da aka caɓa masa ado.

“Yayin bikin, Sarkin Ƙauran Namoda, wanda aka sani da Sarkin Kiyawan Ƙauran Namoda, Dr. Sanusi Muhammad Ahmad Asha, ya naɗa Gwamna Dauda Lawal muƙamin ‘Wakilin Ƙaura,’. An yi masa wannan naɗi ne domin yaba halartar bikin da gwamnan ya yi.”

Sanarwar ta ƙara da cewa, Gwamna Dauda Lawal ya ƙaddamar da babbar ƙofar shiga gari ta Modomawa, ƙofar Ƙauran Namoda mai daɗaɗɗen tarihi tun 1807-1810.

Ga ƙarin hotuna daga wajen bikin: