Maza masu dukan mata

Tare da AMINA YUSUF ALI

Masu karatu barkan mu da sake haɗuwa a wani makon a filinmu mai albarka, Zamantakewa na jaridarku mai farin jini ta Blueprint Manhaja. 

Fatan kun kammala azumi kuma kun yi sallah lafiya. Mun sani cewa mun tafi hutun maganar zamantakewa ta aure a wannan shafi, saboda zuwan watan Ramadan.

Mun yi amfani da lokacin wajen kawo wa mata girke-girke waɗanda za su ƙara ƙawata musu aurensu. To alhamdulillah, mun kammala azumi kuma mun yi sallah lafiya, Allah ya sa karɓaɓɓu ne.

Yanzu za mu ci gaba a kan maudu’in da muka saba kaso muku wato nasiha kan zamantakewa. A sha karatu lafiya. 

Tun kafin azumin nan da ma wasu lokuta bayan azumin nan akwai wasu labarai da suka ɓullo a kan maza masu dukan mata. Har ma an sha tafka muhawara a kan maudu’in a zauruka da dandalan sada zumunci na intanet.

Sai dai kuma sai yanzu na samu lokacin cewa wani abu a kan wannan maudu’in. 

Da farko dai shi duka a zaman aure da maza suke yi wa mata abu ne a al’adance da addinance ma bai kamata ba, kuma abu ne da yake ci wa mata tuwo a ƙwarya. Duk da dai shi duka a gidan aure ba Hausawa suka fi yinsa ba. Wasu ƙabilun na Nijeriya sun fi yinsa.

Sai dai shi ma Bahaushe yana nema ya ara ya yafa. Abin tambaya, me yake jawo duka a zaman aure?

Babban abinda yake jawo duka a zaman aure ba ya wuce zafin zuciya daga ɓangaren namiji. Yayin da matarsa ta yi masa laifi, zuciya ta kufulo shi ya zuciya ya hau dukan ta.

Wani laifin ma da maza suke dukan mace bai kai ya kawo ba. Kuma daga sanda ya tsaga ya ga jini, ma’ana idan ya yi ya ci riba, shikenan ya ga waje. Kullum ana laifi kaɗan, sai ya ce, duka. Wani lokacin ma ba ita za ta kar zomon ba, wani ne kawai zai vata masa rai a can waje, amma sai ya zo gida ya nemi dalili komai ƙanƙantarsa ya rufe ta da duka don ya huce wancan haushi da aka ba shi.

Wani kuma shaye-shaye ne yake kai shi ga dukan mata. Kuma ma fi yawan lokuta zai iya ji mata rauni, wani lokacin ma idan da ƙarar kwana, ta rasa ranta. 

Sai dai kuma a ganina mazan da suke aikata wannan ta’addar ta dukan mata, anya suna da laifi?

Ni dai har ga Allah ban fiye ganin laifinsu fiye da na matan ko na al’ummar gari ko iyaye da dangin matar da nasa ba.

Ɗanadam yana da wata xabi’a ta cigaba da yin abinda yake ko da kuwa mara kyau ne, in dai har zai samu goyon bayan wasu mutane. Ko kuma zai samu wata hujja ya dogara da ita. A ganina, namiji madokin mata ba zai tava samun yin haka ba sai da ƙwarin gwiwa da taimako daga wasu mutane ko wasu abubuwa. 

Da farko ma dai ina mamakin mace ki zauna dafi’an har namiji ya jibge ki, ba ki tavuka komai ba. Daga kin ga ya zuciya ba za ki gudu ki bar wurin ba? Ƙarfinku ma ba xaya ba. Idan kika zauna idan da qarar kwana ma halaka ki zai yi.

Sannan ya miki duka na ɗaya, ya yi na biyu, wataqila ma da na uku. Ke ko baiwar Allah zaman me kike yi a gidan? Na san za ki ce zaman ‘ya’yanki. To amma idan kika bari ya kashe ki ba kya Duniya, wa zai kula da yaran da kika bari? Sai ki yi tunani ki yi karatun ta-nutsu. Kuma idan tarbiyyar yara kike gudu kada ta lalace idan kin bar gidan, shi ya sa kika nace sai kin zauna, to wacce tarbiyya za su koya a wajen ganin ubansu yana dukan uwarsu kullum?

Ko kuma wanne mutunci za ki yi a idon ‘ya’yan ke da ubansu bayan kullum suna ganin yana jibgar ki? Ƙarshe dai su girma su fara harzuqa da ganin ubansu yana dukan ki zuciya ba ƙashi, sai su kasa daurewa su shigar miki ko su zage shi, ko su rama miki dukanki.

Kin ga ƙarshe dai ya vata muku tarbiyyar ‘ya’ya kuma yana neman haɗa su da fushin Ubangiji. Ke kuma a lokacin ba abinda kike buƙata illa yaran su zama masu albarka su tallafe ki, sai ga shi sun vuge da neman fushin Allah wanda zai iya sa rayuwarsu cikin gararin da bala’i. To kinga duk yadda kuka juya, zaman ba shi da wata rana ko alfanu a rayuwarku da ta yaranku. Gara ki arce tun kina da damar yin haka.

Kada ku saurari masu cewa, ki yi haƙuri ki zauna zai gyara. To yaushe zai gyara ɗin? Da wuya madokin mata ya daina fa in dai ba wani ikon Allah ba. 

Masu karatu a nan zan dasa aya a wannan makon. A mako na gaba Insha’Allahu za mu ci gaba daga inda muka tsaya, insha’Allah. Allah ya raya mu zuwa wani makon da rai da lafiya. Na gode.