Majalisar Dokokin Kaduna ta kama hanyar binciken gwamnatin El-Rufai

Daga BASHIR ISAH

Majalisar Dokokin Jihar Kaduna ta kafa kwamiti na musamman domin binciken yadda gwamnatin Nasiru El-Rufai ta gudanar da hada-hadar kuɗi a wancan lokaci.

Kwamitin zai binciki yadda tsohuwar gwamnatin ta ciyo bashi da bayar da kwangila da dai sauransu.

Yayin wani taron jin ra’ayiyin jama’ar gari da aka shirya a ranar Asabar da ta gabata, an jiwo Gwamna Uba Sani na ƙorafi kan tarin basussukan da ya gada daga gwamnatin El-Rufai tun daga 29 ga Mayun 2023.

Gwamnan ya ce abin da ya zo ya tarar bai taka kara ya karya ba don kuwa ko albashin ma’aikata ma bai isa biya ba.

Ya ƙara da cewa, basussukan da ya gada daga tsohuwar gwamnatin jihar sun haɗa da miliyan $587 da biliyan N85 da kwangiloli 115.

Sai dai, a ranar Talata Majalisar Dokokin Jihar ta kafa wani kwamiti na musamman da zai gudanar da bincike kan yadda tsohuwar gwamnatin ta gudanar da hada-hadar kuɗaɗenta daga shekarar 2015 zuwa 2023.