Marubuta sun yi rawar gani cikin Ramadan – Queen Nasmah

Daga ABBA ABUBAKAR YAKUBU

A cigaba da kawo muku tattaunawar da muka yi da marubuta da ƙungiyoyi game da ayyukan da suka gudanar cikin Ramadan, ƙarƙashin ƙungiyoyi da jagorori daban-daban. A wannan makon muna ɗauke ne da tattaunawar da wakilin Blueprint Manhaja Abba Abubakar Yakubu ya yi da wata marubuciya Asma’u Lawal Liman, wacce aka fi sani da Queen Nasmah, shugabar ƙungiyar Moonlight Writers Association. A zantawar da suka yi Nasmah ta bayyana irin shirye-shiryen da suka gabatar da kuma ayyukan da suke yi na jinqƙai da taimakawa mabuƙata, a lokacin azumi da bayansa.

MANHAJA: Mu fara da sanin wacce ce Queen Nasmah?

QUEEN NASMAH: To, ita dai Queen-Nasmah mutum ce kamar kowa, kuma marubuciya ce kamar yadda mutane da yawa suka sani.

Gaya mana tarihin rayuwarki mu ji yadda rayuwa ta kasance miki.

Asalin sunana shi ne Asma’u Lawal Liman. Ni haifaffiyar Jihar Zamfara ce, daga ƙaramar Hukumar qauran Namoda. Na fara karatuna tun daga matakin ajin rainon yara wato Nursery, zuwa firamare, a makarantar Nelson Mandela International School da ke Abuja. Na kuma yi karatun sakandire a Jihar Katsina a wata makaranta da ake ce wa Ulul Albab Science Secondary School Katsina. Na kuma kammala karatuna a matakin Diploma a shekarar 2021, inda na karanci ilimin fasahar injiniyancin gine-gine wato Civil Engineering Technology. Yanzu kuma na cigaba da karatuna zuwa matakin gaba da Diploma wato HND. A ɓangaren karatun addini kuwa na sauke Alƙur’ani Mai Girma a shekarar da na gama makarantar sakandire, sannan na sake maimaita saukar a shekarar da nake shirin gama diplomata.

Wanne abu ne tun tasowarki yake ƙarfafa miki gwiwa a rayuwarki?

Babban abinda ke ƙarfafa min gwiwa a rayuwata shi ne sanin cewa duk duniya babu wanda zai so ka kamar yadda za ka so kanka a rayuwa, kuma babu wanda zai so maka alkhairi kamar yadda za ka so ma kanka. Abin lura a nan shi ne duk wani mataki da za ka hau a rayuwa babu wanda zai mori cigabanka kamar yadda za ka mori kanka. Don haka ka bar ganin ana matsa maka ka yi abu, kowanne abu amfanin kanka ne.

Mene ne ya ja ra’ayinki ki ka fara tunanin yin rubutun adabi?

Ni tun tasowata na kasance ma’abociyar son ƙirƙira ce. Wannan shi ne babban dalilina. Idan zan taƙaita zan ce ina son rubutu ne shi ya fara jefa ni a harkar adabi, wato soyayya ce sila. Soyayyar da nake wa rubutu.

Gaya mana yawan littattafanki da sunayen wasu daga ciki.

Aƙalla na rubuta littattafai za su kai 15, a ciki akwai biyu da ban fitar ba, Jiddan da Mafakar Ruhi. Sannan akwai wasu biyu da idan na saka da su a lissafi sun zama littattafai 17 na rubuta, sai dai har yanzu ban fitar da sunayensu ba.

Littattafan da na rubuta su ne Ayisha, Mrs Bilal, Barrister Muhammad, Cigaban Mrs Bilal, Fayroz, Wani Hanin Ga Allah, Duniyar Asma’u, Bambanci Aqida, Hajna da kuma Saƙar So. Sauran sun haɗa Nasmawallatu Ƴar ƙara’i, Nawa Ɓangaren, Zinariya, Mafakar Ruhi, da Jiddan.

Wanne labari ki ka fara rubutawa kuma wa ya taimaka miki wajen fara sanin ƙa’idojin rubutu?

Littafin Ayisha shi ne littafina na farko da na fara rubutawa, har na gama rubuta shi ban samu taimakon kowa ba. Babu wanda ya taimaka min wajen fara sanin ƙa’idojin rubutu, amma na samu ƙarin ilimi a tsohuwar ƙungiyata ta Golden Pen Writers Association. Alhamdulillahi, ina godiya sosai gare su sosai. Duk da ban jima a cikinta ba, amma tabbas sun ƙara min ilimi akan wanda nake da shi ta fannin ƙa’idojin rubutu. Ko da bayan na bar su ma ban fasa neman ilimi ba, kuma har gobe ina kan cigaba da neman ilimi.

Wanne ƙalubale ki ka fara fuskanta a farkon fara rubutunki?

Ƙalubalen da fuskanta a littafina na farko shi ne rashin mabiya. Amma a cikin ƙalubalen akwai wani abu mai suna darasi da na koya. Na koyi darasin juriya da jajircewa. Tunda na fara rubuta Ayisha har na gama ƙawata kawai ke karanta littafin, amma hakan bai sa gwiwata ta sare ba. Na sake rubuta wani suka zama su biyu. Na sake rubuta na uku, nan ma suka zama mutum uku ke bibiyar littafina. A na huɗu ne suka fara yawa, har dai na kai bana iya ƙirga adadin masu bibiyar littafaina. Alhamdulillahi.

Me ya ƙarfafa miki gwiwa ki ka ga ya dace ki kafa ƙungiyar marubuta ta Moonlight, kuma kafin ita a wacce ƙungiyar ki ke?

Har ga Allah ban taɓa tunanin a duniyar rubutu zan riƙe ko da muƙamin shara ba, babu tsarin rike wani matsayi a raina, amma yanayi ya sa banda zaɓi sai na yi hakan. A lokacin mutane kan min kallon malamarsu, duk da na san ilimina bai kai can ba. Suna min kallon zan iya taimaka musu su cika burinsu na zama marubuta. Ganin yawansu ya sa na yanke hukunci haɗe su wuri ɗaya su koya daga ɗan ƙaramin ilimin da nake da shi a fannin rubutu. Ni da ƴan ƙungiyata a tare muke gudu kuma mu tsira tare. Daga haka ƙungiyar Moonlight Writers Association ta samo asali. Yau gashi an wayi gari muna hararar shekara huɗu da kafuwa idan watan Mayu ya shigo. Kuma kawo yanzu muna da mambobi 27 masu rijista.

Wanne irin tsari ƙungiyar ku take da shi da ya bambanta ta da sauran ƙungiyoyin marubuta adabin Hausa?

To, Alhamdulillahi. Ban san ya tsarin sauran ƙungiyoyi yake ba, amma dai moonlight tana da tsari na taimaka wa gajiyayyu da mabuƙata. Sannan muna da shirye-shirye da muke yi domin riƙe mabiyanmu. A ɓangaren adabi kuwa muna ƙoƙari wajen kiyaye ƙa’idojin rubutu. Kuma nan gaba kaɗan za mu ɓullo da wani tsari wanda zai taimake mu, kuma ya taimaki adabi bakiɗaya.

Idan lokacin azumin watan Ramadan ya zo, marubuta da ƙungiyoyi kan jingine rubutu, su duƙufa kan wasu al’amuran addini, ku a taku ƙungiyar me da me ku ka yi?

E, tabbas haka ne. Mu ma a Moonlight haka muka yi, domin mambobin mu sun jingine rubutu tun sati ɗaya kafin azumi. Sannan mun tsara wasu shirye-shirye guda biyu, da muka gabatar cikin watan azumin da ya gabata. Na farko mun gabatar da shirin ‘Tukunyar Ramadan’ wanda a ciki muka riqa koyar da girke-girke domin mata su amfana. Sannan kuma mun shirya Gasar Kacici-Kacici kan al’amuran da suka shafi ɓangaren addini.

Yanzu da aka kammala azumin watan Ramadan, wanne sabon babi ƙungiyar Moonlight za ta buɗe ga mambobinta da masu bibiyar rubuce-rubucen ku?

Dama Moonlight ta buɗe wa mabiyanta shirye-shirye daban-daban da ake gabatarwa. A ciki akwai shirin ‘ƙalubalenmu’, wanda muke tattauna matsalolin da al’umma suke ciki, mu ga inda mafita take. Sannan muna da shirin ‘Kacici-Kacici’, wanda yake taɓa ɓangaren adabi, da abinda ya shafi addini. Muna kuma da shirin ‘Dandalin Masoya’, wanda muke tattauna abubuwan da suka shafi soyayya. Har yanzu dai ba za mu fasa yin shirye-shiryenmu ba, sai ma ƙari da za mu yi na wani sabon shiri wanda ba mu gama tantancewa ba, in sha Allah.

Shin kina ganin akwai wani tasiri da wannan gasar kacici-kacici da ku ka shirya za ta yi a rayuwar mambobinku har zuwa bayan wucewar azumi?

Sosai kuwa. Shirin Kacici-Kacici da muka yi ya tasirantu sosai a zuciyoyin mambobin mu, domin hakan ya ƙara mana kusanci da son juna. Har ma muna jin kamar kar a gama. Sosai shirin ya shiga rayukan mutane, ba dan shi ne karon farko da muka yi Kacici-Kacici ba, amma yanayin tsarin da muka bi ya taimaka sosai.

Wacce gudunmawa qungiyar Moonlight ke bayarwa ga cigaban al’umma?

Moonlight na bada gudummawa wajen taimakawa mutane da dama, domin ganin sun samu wani abin da za su ci a baki, ko ta fannin suturar makarantar yara, ko kuma littattafan karatu, da sauran su. Duk muna iya ƙoƙarin mu don ganin mun taimaka wa al’umma ta wannan fannin. Yana da kyau mutane su sani ƙungiyar Moonlight ba don rubutu kawai aka kafata ba, tana taimakawa da iya abinda take da shi. Alhamdulillahi.

Sunanki na cikin fitattun marubuta adabi da suka yi shuhura a baya, mai ya sa yanzu aka daina ganin sabbin rubuce-rubucenki?

E, haka ne gaskiya. Na ɗan ja baya a harkar rubutu, amma fa wallafawa ne kawai na daina yi, ina nan ban fasa yin rubutu ba. Lokacin ne dai Allah bai ƙaddara a sake sakin sabon littafi ba. Amma a shekarar nan in sha Allah zan dawo rubutu gadan-gadan. Makaranta a shirya na kusa dawowa.

Wanne albishir za ki yi wa masu bibiyar rubuce-rubucenki na baya?

Idan har masu bibiyar rubutuna a da suna jina, kuma baku manta da ni ba, idan har kun manta ku xauka ni sabuwa ce a gare ku, zan dawo tare da fatan za ku tare ni da soyayyarku kamar yadda kuka nuna min a baya. Sabon littafina zai fara zuwa muku nan bada daɗewa ba, in sha Allah.

Ta wacce hanya ki ke ganin za a inganta yadda ake kasuwancin littattafai don marubuta su riqa samun alheri, kamar yadda masu finafinai ke samun riba sosai?

E, to. Ni ka san na yarda da wata karin magana da ake cewa, Bawa ba ya ci sai rabonsa’. Amma ina ganin hanyar farko shi ne marubuta su qara haɗa kansu kan wanda suke da shi, sannan mu buɗe babbar masana’anta, inda za a iya ɗaukar kowane mutum aikin rubutu a kuma biya shi kamar yadda masana’antar film za ta iya neman marubuci ya mata aiki. Ko kuma ya kasance a ƙungiya akan zaɓi littafi ɗaya da yayi fice a wata ko lokaci bayan lokaci a saya. Amma ina ganin buɗe masana’antar zai fi, domin idan an sayar wa da masana’anta rubutu ko an hayo mutum ya yi rubutu, sai a buga shi a sayar, uwar kuɗi da ribar ta masana’antar ce. Ni da ina da iko da zan iya yin haka.

An ce ke ma kin koma rubutun finafinai, shi ya sa ki ka yi baya-baya da rubutun zube, me yake kawo haka?

Wannan faɗar mutane ce, Rubutu finafinai bai da alaƙa da tsaikon da aka samu a fannin rubutun zube da nake yi. Ni da kaina na zaɓi na jingine rubutu har sai na huta. Kuma duk da hutun da na je hakan bai hana ni yin rubutu jefi-jefi ina ajiyewa ba.

Wanne abu ne ya taɓa faruwa da ke a harkar rubutu wanda ba za ki taɓa mantawa da shi ba?

Gaskiya ba zan iya tuna wani abu da ya faru wanda ba zan manta ba. Amma wataƙila gaba kaɗan za a samu.

Mene ne babban burinki a matsayinki na marubuciya?

Burina shi ne al’umma su ci daga arzikin da Allah ya min ba tare da na ji na gaji ba. Burina shi ne na yi arziqin da zan ɗauki ɗawainiyar maraya, na yi arzikin da zan gina babban asibitin masu taɓin hankali. Burina shi ne na yi arziƙin da duniyar rubutu za su shaida cewa Queen-Nasmah na da burin ɗaukaka duniyar rubutu. Gaskiya ina da babban ɓuri akan rubutu. Allah shi ne shaidata.

Mene ne saqonki ga marubuta da suka ribaci watan Ramadan a ƙarƙashin shirye-shirye da ƙungiyoyin su suka gabatar, yanzu da aka kammala azumi?

Saƙona ga marubuta shi ne a gaskiya kun taka rawar gani cikin wannan wata mai albarka da muka azumta. Ubangiji Allah Ya karɓi ayyukanmu a matsayin ibadarmu. Saƙona ba ga marubuta kaɗai ba ne, ga al’ummar musulmi bakiɗaya ne, Ubangiji Allah Sarkin sammai da ƙassai, mai kowa mai komai, mai yadda ya so a lokacin da ya so ya ba mu ladan wannan wata mai albarka, Ya kuma Allah ka nuna mana wata shekarar da alkhairi. Idan kuma lokacinmu ya zo ubangiji ya amshi baƙuncinmu, ya kuma sa mu cika da imani.

Na gode.

Masha Allah. Ni ma na gode.