
Daga BELLO A. BABAJI a Abuja
Ministan Abuja Nyesom Wike, ya umarci a gaggauta rusa gidaje da wasu gine-gine da suke haifar da tsaiko ga a hanyoyin da ruwa ke wucewa a unguwar Maitama da wasu wurare masu fuskantar barazanar ambaliya a Babban Birnin.
Wike ya bayar da wannan umarni ne bayan aukuwar wata ambaliya a kwanan nan da ta haifar da tsaiko ga harkokin yau da kullum na al’umma a sassan birnin.
Ministan ya bayar da umarnin ne a yau Talata bayan ziyarar sanya ido a yankunan da ambaliyar ta shafa a Maitama, inda wani mamakon ruwan sama ya jefa al’umma cikin matsi da cinkoson ababen hawa.
Akan haka ne ya ba wa hukumomi masu alhakin kula da lamuran gudanarwar Abuja da su hanzarta fara aikin rusau daga yanzu har zuwa ranar Asabar, yana mai cewa za su yi hakan ne ba tare da la’akari da harkokin siyasa ko matsayin waɗanda hakan ya shafa ba, saboda a cewarsa aiki ne da ya danganci kare rayuka da dukiyoyin al’umma.
Wannan na zuwa ne yayin da al’umma suka shiga damuwa kan halin magudanan ruwa a Abuja, haɓakar birni da zargin gine-gine a wuraren da an san hanyoyin wucewar ruwa ne, lamarin da ke jefa makusantan yankunan cikin fargabar ambaliya.
Haka kuma, wannan al’amari ya haifar da suka daga ɓangare Sanata Ireti Kingibe mai wakiltar Abuja a Majalisar Dokokin Ƙasa, wadda ta sha maimaita nuna damuwa kan ambaliya, tare wuraren magudanan ruwa da haɓakar wurare masu fuskantar barazanar ambaliya, amma ta yi zargin cewa dukkan gargaɗi da ankararwa da ta riƙa yi, ba su samu amsa ba daga ministan Abujan.
